‘yan sanda basu isa su hana ni zuwa Kano ba, Inji Kwankwaso

0

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa zuwan da da zai yi Kano ba zai yi don ya tada hankalin jama’a bane, zai zo Kano ne don ya gana da ‘yan uwa da abokan arziki.

Saboda haka bai ga dalilin da zai sa jami’an ‘yan sanda su nemi yi masa katsalandan a wannan ziyara tasa ba.

Binta Sipikin da ta sanar wa manema Labarai matsayar Kwankwaso ta Kara da cewa babu gudu ba ja da baya kan ziyarar Kwankwaso Kano.

” Za mu zo Kano da na’urorin daukan hoto masu yawo a sama da Kan su guda bakwai, sannan manya-manyan gidajen yada Labarai na Duniya zasu taho Kano domin wannan ziyara. Za mu zo mu gana da jama’a sannan mu koma. Ba tashin hankali za mu je yi Kano ba.” Inji Binta.

Idan ba a manta ba rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta gargadi Kwankwaso da ya dakatar da zuwa Kano da ya shirya yi a mako mai zuwa saboda tsaro.

Kwankwaso zai je Kano ranar 30 ga watan Janairu.

Share.

game da Author