YAJIN AIKI: Malamai da El-Rufai sun rike wa juna makogaro

0

A bisa dukkan alamu Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai bai gaji da shan ragargaza ba, ganin yadda ake masa lakabi da “Mai Rusau”, yanzu kuma kuma ana kusa da kiran sa “Korau”, matsawar ya cika alkawarin sa rantsuwar da ya yi cewa duk wani malamin makarantar firamare ko sakandare da ya tafi yajin aiki a yau Litinin to zai kore shi daga aiki.

Sai ga shi malaman na firamare da sakandare na Kaduna a yau sun ajiye alli sun fara yajin aikin sai-Baba-ta-gani domin neman kara inganta musu rayuwar su da kuma sama wa aikin su kariya daga duk wata barazanar masu yi musu bazarana.

Kungiyar Malaman Jihar Kaduna, NUT ce ta kira yajin aikin kuma aka bi umarnin ta a duk fadin jihar.

A cikin haraba da kofar wasu makarantun a Kaduana, babu kowa sai masu gadi, domin dalibai da malaman na su kowa ya yi zaman sa a gida.

Amma a Makarantar Firamare ta Unguwar Mu’azu, an ga malamai a harabar makarantar, amma dalibai babu ko daya.

Can a Kwalejin Rimi Collage kuwa, malaman ba su je ba, amma dai an ga ma’aikatan da ba masu koyarwa ba su na bakin aikin su a makarantar ta sakandare.

Amma kuma a sakandare ta Unguwar Mu’azu da GSS Independence Way, malaman makarantar sun je bakin aikin su, a bisa dalilin su na cewa wasikar sanar da fara yajin aiki da kungiyar malaman jihar, NUT ta raba, ba ta je musu ba.

Sauran makarantu da wakilin mu ya ziyarta kamar GSS Kargi Road, Tudun Wada, LEA Premary School da ke Faki Road a unguwar Tudun Wada, duk fayau su ke babu kowa.

Haka a sauran garuwa ma an amsa kiran yajin aikin sosai.

An dade ana ta kai ruwa rana, tun bayan da aka shirya wa malamai jarabawar gane dakikai a cikin su.

“Babu wata hujjar da zai sa gwamnatin Kaduna ta shata layi ta ce sai wanda ya ci maki 75 ne ya cancanta. Domin ko a Jami’ar Oxford ta Ingila da sauran duniya, idan mutum ya ci maki 70, to babu kamar sa, ya ci “A.” Inji wasu hasalallu.

Rigima tsakanin gwamnatinn El-Rufai da malamai ta samo asali ne tun bayan jarabawar tantance masu kokari daga dakikai da gwamnatin ta ce ta gudanar, inda ta ware sama da dubu 22,000 za ta kora.

Malaman sun je kotu inda su ka garzaya su ka kai karar gwamnati, kuma su ka samu sammacen kada a kore su daga, har sai abin da kotun ta zartas tukunna.

Sai dai kuma sun cika da mamaki, ganin yadda gwamnati ta fara yin watandar takardar sallama daga aiki ga wadanda ta yi niyyar kora, wanda hakan ya sa kungiyar yanke shawarar yafiya yajin aiki.

Sai kuma ba wadannan ne kadai dalilan su na tafiya yajin aikin ba. Malaman na neman gwamnati ta tsayar da ritayar tilas ga malaman sakandare, wadda gwamnatin El-Rufai ta fito da shi,
Su na kuma bukatar a gaggauta biyan malaman firamare su 3,338 kudaden alawus din zirga-zirga na 2015, da kuma sauran malakantu da ba a biya na 2016 da 2017 ba.

Har ila yau, malaman na kuma neman a biya sama da malaman firamare su 15,000 kudaden alawus din albashi na tun daga Yuni, 2015 har zuwa Yuli, 2016 da su ke bi, har yau ba a ba su ba.

NUT ta kara da cewa har yau gwamnati sai kaudin baki, amma ta kasa yi wa malamai karin mukamai da matakan albashi, kuma ta kasa wadatar da kayan inganta koyo da koyarwa a makarantu.

Share.

game da Author