Yadda SSS suka gabatar da El-Zakzaky ga ’yan jarida

0

Lauyan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya bayyana cewa yaudarar malamin jami’an SSS su ka yi har su ka gabatar da shi a gaban ‘yan jarida, domin su yayyafa wa rudanin cewa ya mutu ruwan da zai kashe ji-ta-jitar.

Femi Falana ya ce kai da ganin irin yadda malamin ya gabata a gaban ‘yan jarida a ranar Asabar, kowa ya san ya na fama da matsananciyar rashin lafiya, ba kamar yadda jami’an SSS su ka ce wai ya na cikin koshin lafiya ba.

Lauyan ya ce shi dai ya na nan a kan bakan sa cewa a saki E-Zakzaky ya je ya nemi magani, kamar yadda kotu ta bayar da umarni tun cikin Disamba, 2016.

“Maimakon su amince da rokon da na yi su sake shi, sai SSS su ka ribbaci Sheik El-Zakzaky da su shirya domin gwamnatin tarayya za ta sallame shi bayan an gabatar da shi a gaban ‘yan jarida, domin a tabbatar wa mabiyan sa ‘yan Shi’a cewa ya na nan da ran sa.” Haka Falana ya bayyana.

“Dalili kenan su ka amince da su bayyana gaban ‘yan jarida, wadanda gabadaya minti daya da sakan 20 suka yi a gaban manema labarai, a wani boyayyen wurin da ya ke a killace a Abuja.”

“Sannan kuma sabanin yadda jami’an tsaron ke cewa lafiyar sa kalau, kowa ya ga yadda ya ke dauke da kakkauran bandejin da ke tallabe da wuyan sa, wanda aka daura masa tun wata faduwa da ya yi a cikin Disamba.

“Kafin ya ji ciwo a wuyan sa, ya rasa idon sa na hagu, dalili kenan ma likitoci su ka bayar da shawara cewa a gagguta ficewa da shi waje domin a ceci dayan idon nasa na dama, don kada shi ma ya rasa shi, ya yi biyu-babu. Amma duk haka gwamnatin tarayya ta yi kunnen-uwar-shegu da wannan kira.”

“Abin da likitoci suka bayar da rahoto kan matar sa ya ma fi nasa muni. A kullum ta na fama da matsanancin ciwo sakamakon harsasan da aka harbe ta, su na cikin jikin ta har yau sama da shekara biyu, tun 14 Ga Disamba, 2015, a lokacin da sojoji su ka kai hari a gidan su.”

“To tunda an gabatar da su a gaban ‘yan jarida, me ya rage kuma, ai sai a sake su daga haramtaccen tsarin da ake yi musu bayan Babbar Kotun Tarayya ta ce a sake su.”Inji Falana.

Share.

game da Author