Yadda na shafe shekara 8 ina sana’ar wankan gawa – Gwamnan Oyo

0

Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya bayyana cewa sana’ar wankan gawa ya rika yi ya na biya wa kan sa kudin makaranta, a lokacin da ya ke karatu a Turai.

Gwamnan ya furta haka ne a lokacin da ya ke jawabi a Taron Matasan Kudu-maso-Yamma da aka gudanar a Osogbo a ranar Talata.

Yayin da ya ke kira ga matasa da su kasance masu kyakkawan hangen nesa da aiki tukuru, ya ce sai da ya shafe shekara takawas ya na wanke gawarwaki a kasar waje domin ya tsira da karatun sa kuma ya rika ciyar da kan sa.

Ya ce iyayen sa tun da su ka aika masa da Dalar Amurka 30, ba su kara aika masa da ko sisi ba, har tsawon shekara takwas.

Dalili kenan ya nemar wa kan sa mafita, inda ya nemi aikin da zai rika yi domin ya kai gacin rayuwar sa.

“Na bar Najeriya cikin 1963 na tafi karatu waje. Amma a tsawon shekarun nan takwas, wankin gawa na rika yi domin na biya kudin karatu kuma na ci abinci.”

“Duk lokacin da na koma gida bayan an tashi daga makaranta, sai na rika kuka, ina tuna yawan gawarwakin da na wanke.

“To shugaban mu na masu wankin gawarwaki ya kan ce min na daina tsoro ko fargaba, ya na cewa dama duk sabon-shigar wannan sana’a sai ya fara jin ba dadi a ran sa.

“Shi ya rika kara min kwarin guiwa ya na cewa na zama mai dakakkar zuciya kawai, na rika ayyanawa a raina wadannan gawarwakin kawai na rika yi musu kallon sandararrun kifaye kawai da kankara ta sandarar da su. Watau na daina yi musu kallon gawarwakin mutane.

“Kun gani duk da haka, a cikin irin wannan rayuwa na kasance har shekaru takwas domin kawai na cimma buri na.

Dalili kenan ku ma a yau na ke jaddada muku cewa aiki tukuru shi kadai ne hanyar da za ku tsira da mutuncin ku a rayuwa, har ku kai ga nasara.” Inji Gwamna Ajimobi.

Share.

game da Author