Yadda Gwamnatin Taraba ta umarci ’yan sanda su saki wadanda su ka kashe Fulani

0

An fallasa wata wasika mai shafuka uku da Kwamishinan Shari’a na Jihar Taraba, Yusufu Akirinkwen ya rubuta kuma ya aika wa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Yakubu Babas, inda ya ke umartar sa ko shawartar sa da ya saki wadanda ke tsare a bisa zargin a ake yi musu na kisan Fulani makiyaya da aka yi a jihar.

Wannan wasika ta kara bayyana wasu alamomin zargi da ake yi cewa gwamnatin jihar ce ta dauki nauyin kisan, ko kuma ta na sane za a yi kisan, amma ba yi komai a kai ba.

An dai yi wannan mummunan kisa ne a cikin watan Yuni, 2017, a Mambilla, cikin Karamar Hukumar Sardauna, a jihar Taraba.

Bayan rikicin ya lafa, kwamishinan ’yan sanda Babas, ya furta a kafafen yada labarai cewa mutane 18 ne kacal suka mutu.

Amma Kungiyar Miyetti Allah suka ce adadin ya wuce 18, nesa ba kusa ba.
Sannan jami’an tsaron kuma su ka sun kama wasu da ake zargin su na da hannu a kisan.

Dama kuma kwanaki kadan bayan kisan, Fulani sun fito a ta bakin Miyetti Allah suka ce gwamnatin Taraba da kuma rundunar ’yan sandan jihar na kulla kisisinar boye makasan.

Fulani suka ce, sakin da aka yi wa wadanda ake zargin ya nuna cewa gwamnatin Taraba ce ta nauyin kai musu harin kisan. Amma gwamnatin jihar ta musanta wannan zargi.

Sai dai kuma wata wasika aka fallasa, wadda shi Kwamishinan Shari’ar da kan sa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa shi ya rubuta wasikar zuwa ga Kwamishinan ’Yan sanda, to jama’a da dama na kafa misali da ita cewa da hannun jihar Taraba a kiasan da aka yi wa Fulani.

Amma kuma kakakin ’yan sandan jihar, David Misal, ya bayyana cewa babu hannun jami’an tsaron a sakin da aka yi wa wadanda ake zargin.

Ya ce dukkan su an kai su kotu tun kafin Kwamishinan Shari’a na jihar ya rubuta waccan takarda inda ya nemi a sake su.
Kwamishinan Shari’a na jihar ya ce ya nemi a sake su ne domin a samu zaman lafiya a jihar. Dalili kenan ya ce a sake su.

Wasikar dai an rubuta ta ne a ranar 8 Ga Satumba, 2017, kuma ta nemi a saki dukkan wadanda ake zargin tunda gwamnatin jihar Taraba ta rigaya ta kafa Kwamitin Bincike kafin a kama su.

Sai dai wani lauya kuma mashawarci kan fannin shari’a na Kungiyar Miyetti Allah, ya shaida cewa laifi ne babba rubuta wasikar har a nemi a saki wadanda ake zargin.

Abbo y ace akasarin wadanda aka kama din duk su na da hannu a kisan da aka yi a Mambilla. Don haka ya ce sakin su wani tuggu ne kawai na tauye karfin ikon shari’a da gwamnatin jihar Taraba ta yi.

“Don haka ni a matsayi na, na masanin shari’a, laifi ne a bada umarnin sakin wadanda aka tsare din. Kada ka manta dukkan laifukan da ake zargin sun aikata, manyan laifuka ne fa na kisa da kuma fashi da makami. Kuma da yawansu ma sun aikata wani laifin ne bayan wancan kisan, kuma bayan an rigaya an kafa kwamitin binciken da gwamnatin ta kafa.

‘Ya na aikawa da wasikar, sai kwamishinan ’yan sanda ya umarci a saki wadanda ake zargin, kuma aka sake su. Kwamishinan bai ma bata lokaci wajen sallamar su ba.

“Wannan ai ya nuna cewa akwai wata kullalliya daga bangaren gwamnati domin a kashe mutanen mu a Karamar Hukumar Sardauna.

“To yanzu dai Allah ya tona asirin su, ta dalilin wannan wasika da aka fallasa. Amma ta yaya Kwamishinan Shari’a na jiha zai dakatar da ’yan sanda daga binciken wadanda suka yi mummunan kisa?” Inji Abbo.

To wani abin daure kai shi ne yadda kakakin ’yan sandan Taraba, David Misal ya ce ba su ba ne suka saki wadanda ake zargin, domin su har ma sun gurfanar da su a gaban shari’a.

“An kawo mana wasika a nan Jalingo. Amma fa wasikar nan shawara ce, ba wai umarni ba ne.” Inji Kakakin jami’an tsaron.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa a lokacin da ka aika da wasikar, akwai wasu rikakkun wadanda ake zargi da kisan su hudu da ba a rigaya aka gurfanar a kotu ba.

Ita dai kungiyar Miyetti Allah ta nan a a kan bakan ta cewa an kashe akalla Fulani 800 a Taraba, kuma an ki yin shari’a saboda gwamnatin jihar ta bada umarnin saki wadanda suka yi kisan.

“Mun kai sama da shekaru 150 a Mambilla mu na zaman lafiya da mutane, babu wata matsala. Amma tun da suka fara kashe mu Fulani, sai abin ya sauya.

“Dama tun ma kafin su fara kisan, sun rigaya sun raba wa junan su sunayen wadanda za su kashe. Za ka ji idan sun shiga kauyen Fualani suna cewa, ‘ni zan kashe wane. Wani ma na cewa ni ma ni ne zan kashe wane.’”

“Ai wadanda suka tsira da rayukan su duk suna nan. Wasu da suka yi kisan ma sun tsallake cikin Kamaru sun boye. Amma bayan sun dawo, ‘yan sanda sun kama su, aka kira wadanda suka tsira a Gembu, suka zo suka rika nuna wadanda suka je suka yi kisan.

“Sai ka ga an nuna wannan ko wancan an ce, wannan ne ya kashe min uba ko wancan ne ya kashe min uwa da sauran su.”

Abbo, wanda shi ne Mashawarci Kan Shari’a na Kungiyar Miyetti Allah, ya ce abin mamaki wasu da aka sakin ma sun aikata laifukan su ne kafin ma a kai ga wancan kashe-kashe da ka yi wa Fulani.

“Akwai wanda aka saki, wanda shi kuma Fulani ya yi garkuwa da su, su biyu. Don haka maganar ma a ce ko sharri ko karya mu ke yi a kan gwamnatin Taraba, wannan ba haka ba ne.”

Abbo ya ce su na jiran su ga abin da gwamnatin tarayya za ta yi.

Share.

game da Author