Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa su ne manyan laifukan da suka fi muni a wannan zamanin.
Yayin da ya ke jawabi a taron Kasashen Afrika na 2018 a kan Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Buhari ya ce: “Tabbas cin hanci shi na daya daga cikin manyan laifuka da barnan da ake tabka a doron kasa a wannan zamanin .
“ Ita rashawa riba ce, amma ga wadanda ba su bin ka’idar da doka ta shimfida a yi komai daidai. Dalili kenan ta ke karya duk wani kokari da kowace gwamnati ke yi domin a yi komai a kan ka’ida.”
Daga nan sai ya shaida wa mahalarta wannan taro na 30 cewa ya sha alwashin zai yi iya bakin kokarin sa, kuma zai yi rawar ganin da lailai za a san cewa an fatattaki rashawa da wawurar kudade daga 2018 har ma shekaru nan masu zuwa.