Wata ta kashe mijinta kwanaki 4 da tarewa a Kano

0

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano Magaji Majiya ya bayyana cewa rundunar sa na farautar wata amarya da ta kashe mijinta kwana hudu bayan an daura musu aure.

Ita dai wannan amarya ta zuba wa mijinta maganin kashe beraye ne a abincin sa inda bayan ya gama ci cikin sa ya ko murde cikin dare.

‘Yan uwan mamacin da suka sanar wa ‘yan sanda sun ce zuwa washe garin gobe, dan uwan su mai suna Umar Sani ya rasu.

” A yanzu haka ma’aikatan mu sun bazu ko’ina domin ganin sun kamo wannan yarinya da ta gudu bayan aikata wannan mummunar aiki.”

Abin ya faru ne a unguwar Yakasai Quaters, dake Kano.

Magaji Majiya, ya kara da cewa sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da kananan yara a Kano, da ake zargin ya sace wani dan shekara shida a unguwar Dabai dake karamar Hukumar Gwale.

Share.

game da Author