Wasu mahara sun kashe sarki da mai dakin sa a Kaduna

0

Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kashe sarkin Numana, karamar hukumar Sanga, Gambo Makama da mai dakin sa a daren jiya, Lahadi.

Dan sarkin da ya tsira dauke da raunuka ya ce bayan kashe iyayen sa da maharan suka yi sun Kona gidan su tas.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya tabbatar da faruwar haka sannan ya ce jami’an sa sun fantsama wajen ganin an gano wadanda suka aikata wannan aiki.

A ganawa da manema Labarai da kakakin gwamnan jihar Kaduna Samuel Aruwan yayi a Kaduna yau, ya ce gwamnati ta yi matukar nuna rashin Jin dadin ta kan abin da ya faru. Sannan ta umarci jami’an tsaro da su sa himma wajen zakulo wadanda suka aikata wannan aiki.

Share.

game da Author