Rundunar yan sandan Taraba, ta bayyana cewa lallai an sami tabbacin hari da aka kai wasu kauyukan fulani da ke karamar hukumar Lau.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar David Misal, ya ce an bizine gawakin Fulani hudu bayan harin.
Har yanzu ba a san wadanda suka aikata wannan mummunar aiki ba, inji rundunar ‘yan sanda sai dai wani mazaunin kauyukan da aka kai wa hari ya ce sama da mutane 10 suka bizine bayan harin da aka kai kauyukan a jiya. Ya ce ‘yan kabilar Bachama da Nyandan ne suka kai musu wannan hari kuma suka aikata kisan.
Kallamu Mohammed da ya tsira da ran sa ya ce Allah ne ya sa zai rayu domin duk jikin sa harbin bindiga ne sannan maharan da sauke zargin yan kabilar Bachama da Nyanda ne sun kona musu gidaje kaf.
Discussion about this post