Shugaban Kwamintin Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Rashawa, Itse Sagay, ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Buhari wasika, inda ya shawarce shi kada ya tsaya takara a 2019.
Masanin shari’a Sagay, ya ce wasikar ta Obasanjo, cin fuska ne kuma ba ta dace ba. Ya bayyana Obasanjo da cewa mai bunu a gindi ai ba ya kai gudummawar kashe gobara.
“Ai ni da na ga wasikar Obasanjo, mamaki na yi, har na yi zaton ko dai ba shi ba ne ya rubuta ta. Kai ka ji mutumin da ya kusa rikita kasar nan saboda zafin neman sai ya yi zango na uku, wai shi ne zai baiwa wanda zai yi hasataccen zangon san a biyu shawarar kada ya sake tsayawa takara.
“Ya kamata Obasanjo ya ja girman sa, kuma ya rika mutunta jama’a. na yarda da cewa gwarzo ne, ya yi aiki, ina girmama shi. Amma fa ya dace ya kame kan sa haka nan kafin mutuncin sa ya zube.’’