Yayin da ’yan Najeriya ke tsakiyar halin kuncin tsadar fetur da karin kudin shiga motocin sufuri tun kafin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, a yau kuma an wayi gari Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kara kudin tikitin shiga jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, bayan kaddamar da karin jirage da taragai da ake shirin yi ranar Alhamis mai zuwa.
Amaechi ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan ganawar da ministan ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari a yau Talata.
Ya ce tun tuni su kan su fasinjojin sun amince da cewa ana hawan jirgin arha daga Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce shi da Shugaban Kasa sun tattauna batun karin jiragen da aka samu tare da tattauna cewa za a kaddamar da su a ranar Alhamis.
“Shugaban Kasa ya yi murna da karin jiragen wadanda kawo su zai magance yawan fasinjojin da ake samu da kuma kawar da cuwa-cuwar tikiti da ma’aikatan ke yi.
Ya ce za a ware jirgi daya kacokan wanda zai rika tasowa daga Kaduna zuwa Abuja kai tsaye ba tare da yada zango ko ina ba. Ya na mai cewa shi wannan jirgin zai iso Abuja ne cikin awa 1:15 ko awa 1:20. Ya ci gaba da cewa ’yan Kaduna mazauna Abuja za su iya zuwa aiki a kullum cikin lokaci ba tare da sun yi latti ba.