Kwanan baya da rikicin Fulani da manoma ya rincabe a jihar Benue, mutane da dama sun yunkuro sun a ta neman yadda za a shawo kan matsalar. A nata bangaren, sai gwamnatin tarayya ta ce za ta killace shanun kiwo a wuri guda a kowace jiha.
Idan ba a manta ba, Sanata Hadi Sirika, wanda shi ne ministan harkokin sufurin jiragen sama, bayan an gama taron Majalisar Zartaswa a Fadar Shugaban Kasa, daga baya ya yi magana da manema labarai, inda ya ce za a yi “colony.” Ko da ya ke dai Audu Ogbe ne, Ministan Gona ya fara yin bayanin.
Haka ya fada da kalmar Turanci. To sai inda aka sha bamban, shi ne inda Sirika ya fassara “colony” da ma’anar ‘burtali.’ Amma maganar gaskiya, fassarar ba ta yi daidai ba.
Burtali hanya ce, ko kuma a ce gwadabe, wanda gwamnati tun kafin samun ‘yancin kai ta yi wa makiyaya domin su rika bi da dabbobin sun a kiwo, idan za su tafi kiwo, ko kuma idan sun dawo daga kiwo, ko kuma musamman idan sun yi kaura daga wannan ruga zuwa waccan, ko daga wannan yanki zuwa wancan.
Da ya ke akwai Fulani a fadin kasashen Afrika, wannan burtali za a iya lura da cewa ya na da mahada daga wannan kasa da na makwabciyar ta. Misali, tun a wancan shekaru an tsaya yadda Fulani za su iya tashi tun daga Jamhuriyar Nijar, su shigo Dajin Rugu da ke Katsina da kuma dajin Dajin Zamfara da na Birnin Gwari, har su nausa Dajin Falgore, ba tare da sun shiga gonakin manoma ba. Kai har ma su dangana da Adamawa su tsallaka Jamhuriyar Kamaru.
Sannu a hankali sai duk wadannan burtaloli duk suka bace a doron kasa. Ko dai masu gonaki sun yi musu cin-iyaka, an mayar da su cikin gonaki, ko kuma masu gari da sauran hukumomin gundumomin sun sayar da burtalolin ga manoma.
Kalmar ‘colony’ da gwamnatin tarayya ta yi amfani da ita, ma’anar ta ba burtali ba ce. Ta na nufin a killace shanu wuri daya da nufin tara su domin su rika hayayyafa, ana amfani da naman su, man su, fatar su, kashin su domin a yi taki da shi da kuma kara yawan su.
Wannan tsari da ta ce za ta yi, bai yi wa wasu jihohi dadi ba. Domin sun a gani kamar wata sabuwar barazana ce a killace wasu Fulani a wuri daya, wanda hakan da wuya idan zai iya kawo karshen rikice-rikicen.
Wani abin da gwamnatin tarayya ta kasa yin la’akari da shi, shi ne yadda su Fulanin ake bin su har cikin rugagen su ana karkashe su, sannan a sace musu shanu daga guda daya har zuwa 300 a lokaci guda.
An sace milyoyin shanu a Arewa, kama daga na Fulanin Yobe ta dalilin farmakin Boko Haram, na Katsina, Zamfara, Kaduna da sauran jihohi.
Tambaya a nan, shin barayin shanu ba za su iya shiga cikin ‘colony’ ba, su rika sata shanu sun a kashe makiyaya? Shin su makiyayan ba za su kare dabbobin su daga barayi ba? Idan hukuma ta yi sakaci ana kashe Fulani ana satar shanun su, anya su kuma za su zuba ido kawai?
Zan iya fassara ‘colony’ da kalmar Dangwali, duk da dai cewa ba ta hau daidai ba. Dangwali wata doguwar igiya ce mai tsawo da ake kafawa a garken shanu, a daure a jikin turke, ko turaku.
Daga nan sai a bi a na daura mata igiyar dabaibayin daure shanu a tsakanin duk taku uku zuwa biyar. A haka sai ka ga an killace shanu da yawa, a wuri daya, amma su na daure a jikin doguwar igiyar dangwali daya.
Kalmar ‘colony’ da gwamnati ta bayyana a ta bakin Ministan Ayyukan Gona, Audu Ogbe, ta zo wa mutane bambarakwai, domin tabbas a duk duniya kasar Pakistan ce kadai ke da ‘colony’, ko na ce dangwalin kiwon dabbobi.
Shi wannan dangwalin shanu ko na ce ‘colony’ da ke Pakistan, an gina shi ne a bayan garin Bin Qasim da ke cikin jihar Karachi a Pakistan. Nan ne cibiyar hada-hadar naman shanu, kuma nan ne ake tara madara ana maida ta ta zamani a cikin kwalaye da gwangwanaye, kai har ma kantuna manya-manya ke a wurin.
A wurin kuma akwai manya manyan mayankan dabbobi, da gidajen adana nama masu yawan gaske.
To idan aka yi la’akari da wannan, za a ga su kuwa Fulani kiwata shanun su ne ya dame su, makiyayi daban, mayankar dabbobi da kasuwar su daban. Amma duk gwamnatin Nijeriya ta ce ta ji, kuma ta gani, za ta yi musu dangwali daya, ta killace su wuri guda. Tabdijan!
Audu Ogbe ya ce za a samar wa Fulani da dabbobin su tsaro da kuma ruwan sha da abainci. Tuni ya ce jihohi 16 sun amince sun bayar da filayen da za a kafa ‘colony’ na killace dabbobin.
Shin ko hakan zai yiwu? Za a iya killace su kuma a samar musu tafkuna domin shayar da dabbobin su? Za a iya giggina musu madatsun ruwa? Ciyawa fa idan rani ya yi? Maganar tsaro fa? Yanzu da ake karkashe su ana sace musu shanu, su na samun tsaron kuwa?
Bahaushe ya ce: “Da aka ce wa kare ‘ana buki a gidan ku’, sai ya ce, ‘na gani a kasa!”
Discussion about this post