Tsakanin Fulani da ‘yan Kabilar Bachama; Anyi kashe-kashe ranar Lahadi

0

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukan su kuma an kona gidaje da dama a rikici tsakanin makiyaya da ‘yan kabilar Bachama a kauyen Kikon dake karamar hukumar Numan, jihar Adamawa.

Wani mazaunin kauyen mai suna Ngurigon Yohanna da ya tsira da ran sa ya fadi wa manema labarai cewa a safiyar Lahadin jiya ne wasu Fulani suka kawo wa kauyen su hari inda suka kashe mutane hudu sannan suka kona gidaje da dama.

Ya ce sakamokon wannan hari ne ‘yan kabilar Bachama suka yi gangami da yammacin ranar suka far ma kauyukan Dowayan-Waja da Lure.

” Atakace dai sakamakon wannan hari da ‘yan Kabilar Bachama suka kai babu wanda ya san adadin yawan mutanen da suka sheka lahira.”

Shima shugaban karamar hukumar Numan Arnold Jibila ya tabbatar da harin amma bashi ta masaniyar adadin mutanen da suka rasa rayukan su a harin.

Daga karshe jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda jihar Adamawa Othman Abubakar ya fadi cewa maza biyu da mata biyu ne suka rasa rayukan su a wannan harin sannan mutane da dama sun sami rauni.

Share.

game da Author