TAMBAYA: Shin Matan da ta kashe mijinta zata gaje shi? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, Hakika halin da al-umma ta samu kanta a ciki na cin zarafin ma’aurata ta hanyan cutar da abokin zama harma da kisa. Wannan mummunar dabi’a ce da Allah ya haramtawa musulmi mace ko na miji.

Duk mutumin da ya kashe wani ba zai gaje shi ba, shin miji ne ya kashe matar sa ko matar ce ta kashe mijin ta? Ma-haifi ne ya kashe dan sa ko dan ne ya kashe baban sa? Yaya ne ya kashe kanin sa ko kani ne ya kashe yayan sa? Mace ce ta kashe namiji ko namiji ne ya kashe mace? To, kowane ne ya kashe wanda zai gada, to baida gadon wanda ya kashe a shari’ance.

Duniyar musulunci baki daya tayi hukunci da cewa duk wanda ya kashe mutumin da zai gada, to bai da gadon sa. Imam Malik da Ahmad sun ruwaito Hadisi daga Umar (RA) cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam yace: Wanda ya kashe magajin sa ba shi da gado.

Magaji bai da gado idan ya kashe mutumin da zai gada, kisan ganganci ne, ko na kuskure ne, ko kuma mai kamar ganganci ne. Bugu da kari ma duk wanda ya kashe wata rai kisan ganganci to, shari’a ta kashe shi kawai, don zaman lafiya. Amma idan kisan kuskure ne, to kisan ta wajabta masa:

1- Biyan diyyar rai :kimanin Naira miliyan hamsin da takawas da wani abu (N58,443,639).

2- Kaffara azumi sittin.

3- Haramcin Gado.

4- Haramcin Wasiyya

Ya Allah! Ka tsare wannan al-umma daga munanan halaye. Amin

Share.

game da Author