TAMBAYA: Shin mai yin kasaru zai iya yin sallar la’asar a lokacin sallar azahar ko a’a? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Shin me yin kasaru zai iya yin sallar la’asar a lokacin sallar azahar ko a’a?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugaban mu Annabi
Muhammad SAW.

Matafiyi mai kasaru zai iya hada salloli biyu masu tafiya a lokaci daya, kamar Azahar da La’asar, Magriba da Ishha’i.

Wajibi ne mai kasarun da zai hada salla ya daura niyyar hadin kafin fitan lokacin sallar farko. Kuma wajibe ne ya sadar da sallolin biyu batare da jinkiri ba a tsakanin sallolin.

A kwai hadin salla kala uku kamar haka:

1 – Jam’u SURI: matafiyi zai yi wannan hadin a karshen lokacin sallar farko kuma a dai-dai farkon lokacin salla ta biyu. Za’a yi wannan jam’i ne idan lokacin sallar farko ta sami matafiyi cikin tafiya kuma idan ya tashi don cigaba da tafiyarsa ba zai tsayaba sai bayan lokacin salla ta biyu.

2 – Jam’u TAQDIM: matafiyi zai yi wannan hadin ne a lokacin sallar farko. Za’a yi wannan jam’i ne a lokacin da matafiyi ya ke tsamanin ba zai tsaya ba sai cikin karshen lalurin salla ta biyu koma bayan
shudewan lokacin sallar ta biyu.

3 – Jam’u TA’KHIR: matafiyi zai yi wannan hadin ne a karshen lokacin
salla ta biyu. Za’a yi wannan jam’i ne a lokacin da sallar farko ta sami matafiyi a cikin tafiya, kuma ba ya bukatar tsayawa sai a karshen lokacin salla ta biyu, kafin shudewan lokacin mukhtarin salla ta biyu.

Lalle Hadisi ya inganta a Bukhari da Musulim cewa Annabin tsira
(Sallallahu Alaihi Wa-Sallama) ya yi kasaru, kuma ya hada salloli biyu masu tafiya da lokaci daya a cikin tafiyarsa.

Wato sallar Azahar a hada ta da La’asar, Magariba kuma a hada ta da Isha’i. kuma dukkanin malamai sunyi ittifaki matafiyi zai iya yin kasaru kuma ya hada salloli biyu lokaci daya.

Allah ya sa mu dace. Amin

Share.

game da Author