Wani masinja mai suna Abubakar Shu’aibu da ke aiki a sakandare ta GSS Sabongari, Zaria, ya yanke jiki ya fadi sumamme, yayin da aka damka masa takardar sallama aiki a yau Talata.
Kwakkwarar majiya ta tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai cewa Abubakar ya suma ne da sanyin safiyar yau Talata, bayan ya shafe shekara 11 ya na aiki da gwamnatin jihar Kaduna.
“Mun je wurin aiki a yau Talata, sai aka kira Abubakar Sha’aibu a ofishin Shiyya na Hukumar Kula da Ilimi, inda ya na isa aka damka masa takardar sallama.
“Ya nuna mana takardar bayan ya dawo nan makaranta ya same mu. Sai mu ka ba shi shawara da ya karbi abin a matsayin kaddara ce daga Allah.
“Mu na cikin yi masa nasiha kawai sai mu ka ga ya girde ya fadi kasa, inda nan da nan mu ka yi hanzarin yi masa taimakon-gaggawa. Mu ka daga shi, mu ka kwantar da shi a kan dabe, mu na yi masa fifita. Daga nan ne ya fara dawowa daga hayyacin sa.” Inji wani ma’aikacin makarantar.
Ma’aikacin ya kara da cewa nan take malaman da ke wurin su ka taru, inda su ka yanke shawarar yi masa karo-karon dan tallafin da ya saukaka daga cikin albashin su, domin ya dan rage zafin radadin takaicin korar da aka yi masa.
An ce malaman sun roki shugaban makarantar Sa’idu Liman-Umar da ya dubi girman Allah ya taimaka ya dauke shi aiki na wucin-gadi, inda nan take ya amince. Ya kuma sha alwashin taimaka masa shi ma da dan abin da zai iya kokartawa.
Discussion about this post