Mai martaba sarkin musulmi Sa’ad Abubakar III ya kaddamar da ofishin cibiyar karantar da addinin Musulunci a jihar Sokoto na dindindin.
Cibiyar ta yi shekara 15 tana gudanar da aiyukkanta a wani ginin haya kafin tsohon gwamnan jihar Aliyu Wamakko ya gina wa cibiyar sabuwar ofishi.
Sultan Abubakar ya yaba wa Wamakko sannan ya kuma yi masa godiya kan wannan kyakkyawar aiki da yayi.
Daga karshe wasu limamai biyu Sidi Sidi da Ahmadu Mai-Roba,tare da kwamishinan addinin musulunci na jihar, Mani Katami da shugaban kwamitin kula da aiyukkan wannan cibiya Muhammadu Usman a nasu tsokacin sun yi kira ga sauran attajiran jihar da su yi koyi da abin da Wamakko ya yi cewa hakan zai taimaka wajen tarbiyatar da matasa da koyar dasu addinin musulunci.