Hukumomin Sojojin Najeriya sun bayyana cewa sojoji sun kashe sarkin matsafan ‘yan ta’addar Tivi, Torder Gber, wanda aka tabbatar da cewa shi ne ke bai wa ‘yan ta’addar lakanin asiri.
Sun ce sun kashe matsafin ne an kai farmaci a tsangayar da ya ke tsatsube-tsatsuben sa.
Kakakin Rundunar Sojoji, Sani Kukasheka, ya ce idan ba a manta ba, jami’an tsaro sun bada sanarwar neman sa ruwa a jallo tun cikin Mayu, 2016.
“Bincike ya tabbatar da cewa shi ne ke baiwa ’yan kabilar Tivi masu kashe mutane lakani da sirrin da su ke amfanin da su. Kuma tsangayar sa kan zama mabuyar batagari idan yi fashi. Kuma ya na safarar makamai a jihohin Adamawa, Taraba, Nasarawa da sauran su.”
Sai dai kuma Sani Usman, kakakin na sojoji ya ce sun kashe mugun ne, a lokacin da suka yi kokarin raba shi da makaman da ke gaban sa, shi kuma yak i yarda da hakan.