Burget Kwamandan Bataliyar Sojoji ta 23, da ke Yola, Burgediya Janar Bello Mohammed, ya bayyana cewa su na tsare da wasu mutane 11 da ake zargi dangane da bacewa wani jami’in soja a kauyen Opallo, cikin Karamar Hukumar Ladurde da ke jihar Adamawa.
Bello ya shaida wa manema labarai cewa daga cikin wadanda ake tsare da su din har da Hakimin garin, wanda shi ma ya na cikin wadanda ake zargi.
“Amma mun saki Hakimin a bisa alkawarin da Sarkin Bachama, Honest Irimiya ya yi mana cewa za su zakulo duk wadanda ke da hannu a bacewar sojan.”
Ya kara da cewani zaratan sojoji ke ta bincike a yankin da nufin kokarin gano inda ya ke.
Sai dai kuma rahotanni sun ce mutane sai arcewa suke yi daga kauyen Opallo, saboda gudun kada sojoji su yi awon gaba da su.
Discussion about this post