Rundunar Askarawan Najeriya ta bayyana cewa wasu jami’an ta da ke kan aikin jaddada tsaro a cikin kasa, sun samu nasarar kama wani dillalin bindigogi da kuma wani makerin bindigogin shi ma.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin, Sani Usman ne ya bayyana haka a yau Alhamis, inda ya nuna cewa an kama su ne a rananr Laraba. Ya ce an kama dillalin ne a kan titin Akwangwa, a lokacin ya na kan hanyar sa ta zuwa Saminaka a cikin wata mota kirar Opel Vectra.
Bincike ya nuna cewa dillalin mai suna Mohammed Bello, ya nunfi Saminaka ne wajen wani babban gogarman su, mai suna Damina Saminaka.
Kama wannan dillalin bindigogi ne ya yi sanadin cafke wani makerin bindigogi mai suna Dan Asabe Audu, mazaunin kauyen Angbo cikin karamar hukumar Wamba, da ke jihar Nassarawa.
A lokacin da ake binciken dillalin, sai ya shaida cewa ya sayo bindigogin ne a kan kudi naira 30,000 daga hannun wani makerin bindigogi mai suna Dan Asabe.
Lokacin da sojoji su ka dira gidan Dan Asabe a kauyen Angbo, an same shi da kafa wata ‘yar masana wadda ya ke kera bindigogi kuma ya ke saidawa ga masu aikata munanan laifuka.
Discussion about this post