Bismillahir Rahmanir Rahim
Ya ku bayin Allah! Ina yi maku wasiyya da ni kaina da jin tsoron Allah Mai girma da daukaka. Domin tabbas, babu tsira a nan duniya da gobe kiyama face sai da tsoron Allah, kuma tsoron Allah shine ginshiki da tushen dukkan wani alkhairin duniya da na Lahira.
Ya ku bayin Allah, ya ku ’yan Najeriya! Ya kamata mu sani, kuma mu tuna cewa a halin yanzu, kullun muna ta kara fuskanta da kusantar kakar zaben 2019, ga wanda Allah yayi wa yawancin rai daga cikin mu. Don haka, idan ba mu ji tsoron Allah ba, muka yiwa kan mu kiyamul laili, muka yi abin da ya kamata na zaben nagartattun shugabanni masu imani da tsoron Allah, a kowane matakin shugabanci, to ina mai tabbatar maku (Allah ya kiyaye) da cewa abin da muke ji ko gani a yau na bala’in talauci, yunwa, kunci da tsadar rayuwa, na tashin farashin kayayyaki, da rashin iya shugabanci, rashin ayyukkan yi ga matasan mu, yin saku-saku da muhimman al’amura, gasa wa talaka aya a hannu, wulakanta ma’aikata, tozarta su da cin mutuncin su, da rashin daukar shawara, da rashin ababen more rayuwa da talakawa za su amfana da sauransu, da taurin kan masu mulki, wallahi duk zai zama wasan yara. Kuma ba korafi ba, wallahi idan ba mu yi hankali ba sai munyi mummunan dana-sanin da bamu taba yi ba. Allah ya sawwake, amin.
Ya ku jama’ah! Yanzu kenan, suna neman a sake zaben su, suna neman kuri’un jama’ah, amma sun mayar da talakawa ba bakin komai ba, ina ga sun sake dawowa mulki, a lokacin sun tabbatar da cewa suna zangon karshe na mulkin su, sun kammala ba za su dawo ba?
Gashi nan dai ya bayyana a fili karara, duk abin da muke ta kokarin gaya wa mutane ya fito baro-baro. Kowa na kallo da jin abin da ke gudana a wannan kasa tamu mai albarka Najeriya. Dama kuma sun ce JIKI MAGAYI. Saboda haka, yanzu ya rage namu, kodai mu sadaukar da duk abin da Allah Ya hore muna na ilimi da dukiya da karfi da lokaci da wayo da dabara da hankali da gogewa, iya siyasa da sauransu, mu samar da shugabancin da dukkan mu zamu amfana, talaka yasan ana yi da shi, ‘yan kasa su wadata, arziki ya yalwata ko’ina, kayan masarufi su samu, ayi maganin zaman banza ga matasan mu, don samun ingantaccen tsaro, zaman lafiya, ci gaba mai dorewa; mu ceto kasar nan daga shugabanci na rashin kwarewa da dukkan mu muka shaida, ko kuma dukkanmu sai mun yi dana-sani.
Idan muka ci gaba da zama wawaye, makafi, dibgaggu, susutai, marasa kishin kasa, marasa kishin al’umma da kawunan mu, muka ci gaba da yarda da farfagandar karya, to ya rage namu.
Saboda haka, ’yan siyasa, sarakuna, limamai, masu wa’azi, fastoci, ma’aikatan gwamnati da shugabannin addini Musulmi da Kirista da ’yan kasuwa da shugabannin al’umma da talakawa da jami’an tsaro, ku sani hakkin ceto kasar nan ya rataya a wuyan dukkanin ku. Ku manta da kwadayin abin duniya, ku manta da duk wani bambance-bambance, ku manta da maganar bambancin jam’iyya, ku manta da duk wata farfagandar karya da shirme, mu hadu mu yi aiki tare, domin ganin wannan kasa tamu mai albarka ta dawo mai mutunci, mai yalwar arziki da zaman lafiya, hadin kai, da kwarjini a idon duniya.
Ku sani, shi bala’i da talauci da masifa, da yunwa, da kunci da rashin biyan albashi, da rashin hanyoyi masu kyau, da rashin magani a asibiti, da rashin ingantattun ruwan sha, da rashin ingantaccen ilimi, da rashin tsaro, duk babu ruwansu da ko kai wane ne. Babu ruwansu da kai Musulmi ne ko Kirista, babu ruwansu da yaren ka ko jiha ko yankin da ka fito.
Ya ku ’yan Najeriya! Don Allah ku kalli yadda kasarmu ta zama a yau, Ku kalli yadda abinci ya gagari magidanci, mutane suna ta kashe kawunan su saboda talauci da kunci, ku kalli yadda talakawa suka kasa daukar nauyin ilimin ‘ya ‘yan su, ku kalli yadda mutuncin jama’ah ke ta zube wa, an mayar da mutane mabarata, ‘yan maula, maroka, mayunwata da karfi da yaji. An rufe iyakar kasa (wato boarder), kuma kasar nan in banda yaudarar kai, mun san cewa ba tada karfin ciyar da kanta, ba ta da karfin dogaro da kanta. Kuma an ce za’a fitar da abincin mu zuwa kasashen waje, alhali mu gida bamu koshi ba, muna cikin yunwa. An rike arzikin da Allah ya azurta kasa da shi, an ki a saki arzikin da Allah ya hore wa kasa domin kowa ya amfana. Ku kalli yadda ake tafiyar da shugabanci, sakamakon sakaci, rashin tausayi, rashin imani, rashin daukar shawarwari na kwarai, da rashin iya shugabanci. An sakar wa wasu mutane tsiraru harkar gwamnati, an wayi gari sai abinda suka ga dama ake yi. Mutane sun sadaukar da lokacin su, dukiyar su, rayukan su, ilimin su, da duk abinda Allah ya hore masu, domin kawar da bakin mulkin gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan, domin suna ganin ta yi masu ba dai dai ba, babban burin mutane shine Muhammadu Buhari ya zama Shugaban kasar Najeriya, wasu sun mutu, wasu sun rasa hannu ko kafa, wasu sun samu matsala da mutanen su duk saboda Buhari. Talakawa sun bashi gudummawar kudaden su, amma sai gashi yau an wayi gari mutane suna ta dana-sanin abun da suka yi, don sun gano wannan gwamnatin ba abun da zata iya tabuka masu. Canjin da aka yi alkawarin cewa za’a samar masu ashe ba da gaske ba ne, ashe bugi ne, ashe yaudara ce, ashe karya ce.
Ko maganar yaki da cin hanci da rashawan da ake magana, kawai mutane sun gano ashe duk siyasa ce. Domin sai abokan adawa kawai ake yiwa bita-da-kulli. Amma shafaffu da mai, sai abun da suka ga dama suke yi.
Shin ya ku jama’a, za mu ci gaba ne da dora maslaharmu a saman maslahar al’umma baki daya, don kawai tsoron wasu mutane, ko don gudun zagi? Shin Allah bai umurce mu da mu zama masu adalci ba? Shin idan gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan tayi ba dai-dai ba munyi magana, wannan ma idan ta kauce hanya ba za mu zama adilai mu fito muyi magana ba, kamar yadda muka yi wa waccan gwamnatin? Ta yaya za mu yi ta cika masallatai da coci-coci kullum da sunan ibada, da sunan mu masu addini ne, da sunan mu na Allah ne, amma duk yana neman ya zama na banza, yana neman zama munafunci, saboda nuna kabilanci da bangaranci. Kullun mu ne kan hanyar Makkah da Madinah domin yin Hajji da Umarah. Kullun mu ne kan hanyar Jerusalem domin yin Ibadah. Amma mun kasa zama adilai, da zamu yiwa kowa adalci.
Mun kasa hada kai mu tabbatar da shugabanci nagari da kowa zai amfana a kasar mu, an wayi gari kullun kasarmu na neman ta zama abin dariya a idon duniya? Shin mun manta cewa dukkanin mu za mu mutu mu bar abin da muka tara a nan duniya ne? Mun manta ne za mu tashi a gaban Allah gobe kiyama mu amsa tambayoyi a kan yadda muka aiwatar da rayuwar mu a duniya ne? Haba ‘yan uwana ‘yan Najeriya masu albarka, wai shin don Allah me yake damun mu ne?
Ya ku ’yan Najeriya! Ku sani, lallai shekarar 2019 idan Allah yasa muna raye, ita ce shekarar da za mu gane cewa shin mun yi hankali ko kuwa har yanzu muna nan gidadawa, wawaye, sako-tumaki-balle jakai? Ita ce shekarar da za mu gane, shin mun koyi darasi a jikin da muke ji da bakar wahala da tsadar rayuwa, da tsadar kayan masarufi da muke fama da su, ko har yanzu ba mu gane komai ba? Ita ce shekarar kwatar kai, ita ce shekarar da in har ba mu canza wannan bakin canji a wannan kasa ba, to, babu lokacin da za mu iya samar da wani abin azo a gani. Kuma sai dai muce Allah ya kiyaye!
Ya ku ’yan Najeriya! Lallai mu sani, gyaruwar al’umma ta ta’allaka ne a kan gyaruwar shugabannin ta, kuma lalacewar al’umma ta ta’allaka ne a kan lalacewar shugabannin ta. A duk lokacin da shugabanni suka zama na kirki, masu kishin kasa da al’ummarsu, masu shawartar mutanen kirki, masu daukar shawara, masu tausayi da imani, to ana sa ran mutanen kasa ma su zama na kirki. Haka duk lokacin da shugabanni suka zama na banza, tambadaddu, masu yin saku-saku da al’amurra, wadanda basu iya tabuka komai a kan muhimman al’amurra, wadanda zasu kasa cika wa jama’ah alkawurran da suka daukar masu na samar da kyakkyawan canji, to lallai ‘yan kasa ma haka za su kasance. Domin ai a inda akuyar gaba ta sha ruwa, dole ta baya ma idan ta zo nan za ta sha. Shi yasa Musulunci ya ba da muhimmanci sosai a kan sha’anin shugabanci, ya nuna cewa shugabanni dole ne su zamo mutanen kirki ba ashararai ba, adilai ba azzalumai ba, su zama masu iya daukar matakin da ya dace, a duk lokacin da ya dace, kuma ko a kan wa ya dace. Su zamanto su ke tafiyar da ragamar mulkin su, ba wai su sakar wa wasu tsirarun mutane ba. Yin haka zai sa zaman lafiya da ci gaba da arziki da wadata da walwala su yawaita a kasa, soyayya da kaunar juna su watsu, sanadiyyar haka sai a kawar da duk wata kiyayya a cikin zukatan ‘yan kasa, sai ya kasance jama’a basa tunanin an mayar da su saniyar ware, domin suna da gwamnati mai bai wa kowa da kowa hakkin sa, mai sauraren kowane bangare na al’ummah.
Musamman ma mu ‘yan arewa, ya kamata mu shiga taitayin mu, ya kamata muyi karatun ta natsu, ya kamata mu farka daga dogon baccin da muke yi, mu tambayi kawunan mu, shin don Allah arewa ta amfana da wannan mulkin kamar yadda bangaren yarbawa suke amfana? Shin Bola Tinubu yafi duk wani Dan siyasar arewa ne? Shin kuri’un da Buhari ya samu a arewa ya same su a yankin yarbawa ne? Kuma shin me yasa ne ministan kudin nan (finance minister) take kokarin wulakanta arewa da ‘yan arewa da hadin bakin su Tinubu da ‘yan uwanta ‘yarbawa, amma Buhari yayi shiru yana kallo ya kasa cewa komai? Abun da ya faru kwanan nan na korar Munir Gwarzo (Dan Arewa) daga aiki don ya dauki matakin da ya dace akan kamfanin mai na su Tinubu, Wato Oando, ya isa misali. Sannan matar nan (ministan kudi), idan aiki ya shafi arewa sai ta ki fitar da kudi domin ayi aikin. Amma idan aiki ya shafi yankin su na yarbawa sai ta fitar da kudi nan take. Kuma duk muna kallo munyi shiru!
Amma kwanan nan gwamnatin Buhari ta hannun Port Authority, ta wulakanta kamfanin Dan arewa, Alhaji Atiku Abubakar, wato Intels, amma duk bamu damu ba. Sai gashi an cire Dan arewa daga mukaminsa, saboda ya dauki matakin da ya dace a kan kamfanin su Tinubu. Ayi dai mu gani. Wallahi duk abunda akeyi Allah na kallo, kuma zai yi sakamako. Kuma mu ma muna kallo.
Ko maganar da gwamnatin Buhari take yi na samar wa matasa aikin yi na N-Power, don Allah mu bincika, su waye suka fi amfana? Shin ‘yan kudu ko ‘yan arewa? Me yasa muke yaudarar kawunan mu ne? Me yasa ba zamu fadawa juna gaskiya ba? Me yasa zamu munafunci kawunan mu? Haba, Allah fa yana kallon mu! Sannan don Allah ku lura da kyau, za ku ga cewa, duk wani al’amari na ‘yan arewa Buhari baya bashi wani muhimmanci, yafi bada muhimmanci ga sha’anin ‘yan kudu. Aure ne, mutuwa ce, ta’aziyyah ce, jaje ne, ziyara ce, taron harkokin Addini ne, sam na ‘yan uwansa ‘yan arewa da suka sadaukar da rayukan su saboda shi, bai dame shi ba. Amma ku kalli yadda mataimakin sa Osinbajo yake shiga jama’ar sa don Allah! Abun mamaki!!
Ko hayaniyar da ake ta yi da murnar Buhari ya ziyarci Jahar Kano ai shirme ne. Domin da yaya har ya amince yayi ziyarar? Ta yaya aka shirya ziyarar? Ba sai da aka takura masa, aka tursasa masa, surutu da maganganun Kanawa da korafe-korafen su sun game ko’ina, cewa su ne jahar da suka fi bashi kuri’u a zaben 2015, amma ya manta da su, kuma gwamnatin sa bata yi masu komai ba, sannan aka bashi shawara cewa ya kamata yaje Kano, sannan ya amince ya kai ziyarar? Saboda yasan cewa zaben 2019 na zuwa? Kuma yana kwadayin kuri’un su? Don Allah ba haka aka yi ba? To me za’a gaya muna kuma? Kuma don an mayar da ‘yan arewa mayunwata, an talauta su, an jefa su cikin yunwa, sun rude, sun dimauce, wai sai da Buhari zai kai ziyara Kano sannan aka bi gidajen talakawa, gari-gari, kauye-kauye, ana ta raba masu shinkafa da kudade, don asa su manta da bata masu rai da aka yi, aja hankalin su akan su manta da fushin su, su fito su tarbi Buhari. Bayan motocin safa-safa (Bus-Bus) da aka tsara, aka tura anguwa-anguwa, gari-gari, kauye-kauye, domin su kwaso mutane, kuma su mayar da su, bayan kudin abinci da na kashewa da aka raba wa mutane. Haba! Muji tsoron Allah mana!!
Dama ance wani Dan siyasar kudu ya taba fada cewa:
“KU MANTA DA ‘YAN AREWA, DUK YADDA AKA ZALUNCE SU, DUK YADDA AKA BATA MASU RAI, DUK YADDA AKA SA SU FUSHI, DUK YADDA AKA TURSASA MASU, DUK YADDA AKA CUCE SU, DUK IHUN SU, DUK SURUTUN SU, DUK WANI KORAFIN SU, TO KAMAR KAJI SUKE, DA AN WATSA MASU KUDI ZA SU MANTA DA DUK ABINDA YA FARU, ZA SU MANTA DA DUK ABINDA KAYI MASU, ZA SU BI KA Diiiii, KAMAR YADDA KAJI SUKE YI IDAN AN WATSA MASU TSABA!”
Shekaru masu yawa, amma gashi wannan magana tasa tana neman ta kasance gaskiya. Allah ya sawwake, amin.
Hakika Annabi (SAW) ya ba da labari cewa; yana daga alamomin tashin Alkiyama; ya kasance ana shugabantar da mutanen banza, jahilai, wadanda ba sa neman shiriya da Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (SAW), kuma ba sa jin nasiha, ba sa wa’aztuwa, ba sa kwatanta adalci a tsakanin ’yan kasa kuma ba sa daukar shawara, kuma wadanda za su dora mutanen da basu dace ba a kan mukaman gwamnati. Su daga wa wasu kafa a mulkin su, wasu kuwa a takura masu.
Imamu Ahmad da Imam Al-Bazzar sun ruwaito Hadisi daga Jabir dan Abdullahi (RA), ya ce; “Lallai Annabi (SAW) wata rana yace wa Ka’ab bin Ujrata (RA): “Allah Ya tsare ka, Ya kiyaye ka, ya kai Ka’ab daga riskar shugabancin ashararai, wawaye; sai Ka’ab ya ce: “Mene ne shubagancin ashararai, wawaye, ya Manzon Allah?” Sai Annabi ya ce: “Wasu shugabanni ne da za su zo nan gaba, ba sa bin shiriya ta, kuma ba sa bin tafarki na. Saboda haka duk wanda ya gaskata su a kan karyar su da yaudarar su, kuma ya taimake su a kan zaluncin su, to, ba ya tare da ni, kuma nima bana tare da shi, kuma ba zai taba shan ruwan tafkina ba. Kuma duk wanda bai gaskata su a kan karyar su da yaudarar su ba, kuma bai taimake su a kan zaluncinsu ba, to wadannan suna tare da ni, kuma ni ma ina tare da su, sannan za su sha ruwan tafkina.” Annabi (SAW) ya ci gaba da cewa:”Ya Ka’ab bin Ujrata! Ka sani, shi azumi garkuwa ne, kuma sadaka tana kau da zunubi, Sallah neman kusanci ce zuwa ga Allah, ko kuma hujja ce. Ya Ka’ab bin Ujrata! Ka sani duk wata tsoka da ta ginu da haram, to har abada ba za ta shiga Aljanna ba, kuma wuta ita tafi cancantar ta. Ya Ka’ab bin Ujrata! A kullum mutane suna yin sammako, akwai wanda zai sayar da rayuwarsa, akwai kuma wanda zai ’yanto ta, ko ya halakar da ita.” (Ahmad da al-Bazzar ne suka ruwaito)
Ya ku mutane! Ku sani, shi mutumin banza, jahili, shine mai karancin hankali, mai karancin tunani, mara hangen nesa, mai rauni, wanda ko kansa ba zai iya shugabanta ba, balle ya shugabanci wanin sa. Mara daukar shawara, mai rike arzikin kasa, mai kuntatawa mutane, marowaci, mara tausayi, mai tursasawa jama’ah, mai tsananta masu, mara imani. To ’yan uwa, irin wannan mutum ta yaya za ayi ya iya shugabancin mutane kusan miliyan dari biyu? Koda yake idan ’yan kasa suka yi sakaci zai iya yi, amma kasar kuwa za ta susuce ta tabarbare ta lalace, kamar yadda muke gani a yau! Allah ya kiyaye!! Amin.
A wani Hadisin, Annabi (SAW) ya ce: “Alkiyama ba za ta tsayu ba har sai ya kasance munafukan cikin al’umma da wawayenta su ne suke yin shugabanci.” (Dabarani ne ya ruwaito)
Munafukai da wawaye za ka same su masu karancin imani, masu karancin tsoron Allah, makaryata, jahilai, azzalumai, mayaudara, barayi ko masu ba barayi kariya saboda ‘yan jam’iyyar su ne ko saboda wata maslaha ta su ko ta wasun su. Marasa tausayi, masu tsanani, masu jefa al’umma cikin kunci, yunwa, talauci da rashi, masu yin sanadiyyar karyewar arzikin mutane, marasa daukar shawarar masana, wadanda maslahar kawunan su kawai suka sani, sai ta ’ya’yansu da iyalansu da abokansu da ‘ya’yan jam’iyyar su. Babu ruwansu da sha’anin daukacin talakawa da al’umma.
Ya ku bayin Allah! Lallai idan aka wayi gari shugabanni suka kasance ashararai, susutai, marasa daukar shawara, mutanen banza, jahilai, wawaye kuma marasa kan gado, to, lallai al’amari zai lalace! Sai a wayi gari ana girmama mutanen banza a gwamnati, ana wulakanta mutanen kirki. Ko a kusanto da wadanda sam basu cancanta ba, a nesantar da wadanda suka cancanta. Ayi watsi da mutanen da dasu aka fara tafiya, dasu aka sha wahala, a kusanto da wadanda sam basu sha wahalar komai ba, kai hasali ma, su makiyan gwamnatin ne, amma shi shugaban bai gane ba. Sai ka ga an yarda da mayaudara, a wulakanta masu amana, ya kasance jahilai marasa mutunci, tsageru, ’yan ta’adda da suka kware wajen iya cuta da magudi da sharri, da munafunci, su ne masu fada-aji a gwamnatin. Masana kuwa, dattawa mutanen kirki ba su da bakin magana, kuma ko sun yi ma, to ba ta da wani tasiri da matsayi a wurin gwamnatin, saboda gwamnati ce mai goyon bayan ’yan iska, gwamnati ce mai goyon bayan barayi, ’yan ta’adda, mashaya jinin dan Adam, ’yan giya, marasa mutunci. Ta na goyon bayan su a fakaice amma jama’a ba su gano hakan ba.
Babban malami Imam ash-Sha’abiy (RH) yana cewa; “Alkiyama ba za ta tsayu ba har sai an wayi gari ilimi ya koma ana kallonsa jahilci, jahilci kuma ana kallonsa ilimi.” Wannan duk zai faru ne a zamanin da al’amura suka birkice, suka lalace, suka rincabe aka rasa shugabanni nagari. Idan ba su da lafiya su da ‘ya ‘yan su, su tafi kasashen waje ayi masu magani, talakawa kuwa su da ‘ya ‘yan su ko oho, sai dai su mutu. Saboda babu ingantaccen asibiti da talaka zai tafi, domin duk wadanda ake dasu a kasar, sun mutu basa aikin da ya dace. Karatun ‘ya ‘yan su a kasashen waje ne, sun ki su gyara kuma su inganta makarantun kasar mu domin al’ummah su amfana.
Annabi (SAW) ya fada a Hadisin Abdullahi dan Umar (RA) cewa:
“Lallai yana daga alamomin kusantowar Alkiyama; za a dankwafar da mutanen kirki, kuma a daukaka mutanen banza, ashararai.” (Imam Hakim ne ya ruwaito a Al-Mustadrak)
Ya ku ’yan Najeriya! A yau duk wanda yake raye shaida ne shi a kan cewa lallai duk abin nan da Annabi (SAW) ya ba da labari shine yake faruwa. Domin an wayi gari mafi yawan wadanda ke shugabantar mu, face ‘yan kadan daga cikin su, ashararai ne.
Saboda haka ya zama wajibi a gare mu kowa ya yi kokari ya ba da gudunmawa gwargwadon ikonsa, don ya zamo wadanda za su shugabance mu a nan gaba, (musamman a zaben 2019) da muke fuskanta idan da yawan rai, mutanen kirki ne. Sannan wallahi maganar ayi SAK ta kare, kowa halin sa da abinda ya tabuka wa jama’a shine zai fishshe shi. Maganar a laba a bayan Buhari a cuci al’umma ya kare da ikon Allah. Dukkanin mu dai shaida ne, mun ga illar yin SAK da sharrin sa, da rashin alfanun sa. Ko wannan wahalar da wannan aya da wadannan gwamnonin suke gasawa mutane a hannu ya isa yasa mu gane illar cewa ayi SAK da kuma sharrin sa. Dubi yadda gwamnonin nan suke abun da suka ga dama, Buhari yaki daukar kwakkwaran matakin da ya dace, sai dai ya lallashe su, saboda yana kwadayin ya dawo kan mulki, kar su kawo masa cikas. Shin muna ganin gwamnonin nan zasu iya yiwa mutum irin Obasanjo haka, ba tare da ya sauki mataki a kan su ba? Amma dubi yadda suka raina Buhari, don sun san cewa baya iya yin komai, suna da masaniyar cewa baya iya daukar ko wane irin mataki a kan su! DON HAKA WALLAHI BABU WANI MAGANAR SAK, CHANCHANTA SAK KAWAI!!
’Yan uwana ’yan Najeriya! Mu sani, wallahi lokacin yin shiru ya wuce, ba zai yiwu ba a ce majorati mutanen banza ne ke jagorantar mu. Mu sani, dukkanin mu Allah za ya kama mu da laifin rashin tabuka komai kan samar wa al’umma nagartattun shugabannin siyasa. A yau dukkanin mu shaidu ne a kan irin halin da kasar mu da yankin mu mai albarka na Arewa suka shiga, saboda rashin shugabanci nagari. Shugaban kasa dan arewa ne, to amma don Allah wane yanki ne yafi talauci, rashin aikin yi da matsaloli a kasar nan idan ba arewar ba? To abin da ya faru dai ya riga ya faru, yanzu abin tambaya shi ne; me muke yi domin kokarin samar da shugabanni na kwarai masu amana, masu tausayi da kishin talakawansu a nan gaba? Ko har yanzu barci muke yi ne ba mu farka ba?
Ya ku bayin Allah! Mu sani lallai asalin shugabanci shi ne; a shugabantar da wanda ake ganin ya dara kowa ilimi da adalci da gaskiya da amana da koshin lafiya da rashin nuna bambanci ga ’yan kasa, mai kokarin hada jama’ar kasa da rashin son kai, mai kishin kasa kuma gogagge, gwarzon namiji, jarumi, mai iya daukar mataki cikin lokaci, mai sakin hannu, mai kyauta, mai alkhairi, mai kokarin samar da arziki ga ‘yan kasa da sauransu. To amma a yau abin ba haka yake ba, domin mafi yawanci, fasikai, mutanen banza, ashararai, mayaudara, mashaya, barayi, wadanda ba su san kimar dan Adam ba, masu kuntatawa da tsanantawa talaka, masu rike hannu, sune ke shugabantarmu. Saboda suna da kudi, ko don dangartakar su, ko wani matsayi da suke da shi, ko saboda tsabagen rashin kunyar su, ko don ’ya’yan manya ne su, ko don farin jinin su, amma wallahi ba don cancanta ba. Duk wannan saboda lalacewar al’amura ko kuma saboda mutanen kirki na gaskiya sun yi saranda, sun rungume hannuwa, sun zama matsorata, sun mika wuya, sun ce su babu ruwansu da siyasa, sun yarda mutanen banza sun ci su da yaki.
Ya ku ’yan Najeriya! Awfu bin Malik (RA) ya ruwaito Hadisi cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce:
“Mafifitan shugabanninku su ne wadanda kuke kauna kuma suke kaunarku, kuke yi masu addu’ar alheri, su ma suke yi maku. Sannan mafi lalacewar shugabanninku, sune wadanda kuke fushi da su, suke fushi da ku, kuna la’antarsu, su na la’antarku.” (Muslim ne ya ruwaito)
Saboda haka ya ku al’umma! Wallahi ya zama wajibi a gare mu, manyan mu da kananan mu, shugabannin siyasar mu da sarakunan mu da shugabannin addinan mu da manyan masu kudin mu da ’yan kasuwar mu da ’yan bokon mu da talakawan mu da jami’an tsaron mu da ’yan jaridar mu da duk wani mai ruwa da tsaki game da samar da shugabanci nagari a kasar nan, mu hada hannu da karfi mu ga cewa lallai wannan kasa tamu mai albarka Najeriya, ta samu shugabanci nagari, irin wanda kowa ke bukata, domin samun zaman lafiya da hadin kai. Idan ba haka ba, wallahi kashin mu ya bushe, kuma dukkanin mu Allah zai kama mu da laifin yin sakaci, gobe kiyama.
Saboda haka mu ji tsoron Allah! Ya ku muminai mu koma ga Allah! Mu nemi kusancin Mahaliccinmu. Mu roki Allah shiriya da tabbatuwa a kan gaskiya komai dacin ta, mu tuba zuwa ga Allah baki daya, ko ma samu rabauta.
Ya ku bayin Allah! Lallai kamar yadda kuka sani ne, daga cikin abin da hudubarmu ta yau take tsokaci a kai shine cewa; “Ba za ka taba samun mutanen kirki masu gaskiya suna zabe ko goyon bayan zulunci da azzaluman shugabanni ba.”
Ya ku bayin Allah masu girma! Mu sani, Allah (SWT) Ya yi umarni da adalci da goyon bayan adalai a duk inda suke, kuma Ya yi hani da zalunci da goya wa zalunci da azzalumai baya a duk inda suke. Allah Ya fada a cikin LittafinSa Mai girma cewa:
“Lallai Allah Yana yin umurni da adalci da kyautatawa da umarni a bai wa ma’abucin zumunta, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci. Yana yi maku gargadi, tsammaninku kuna tunawa.” (Nahli: 90)
Kuma Allah Yana cewa:
“Kada ku karkata zuwa ga (ku goyi baya/ko ku zabi) wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku. Kuma ba ku da wadansu majibinta ban cin Allah, sannan kuma ba za a taimake ku ba.” (Hud:113)
Ya ku Musulmi! Lallai cikin wadannan ayoyi masu girma, mun ga yadda Allah Ya umurce mu da tsaida adalci da kuma cewa kada mu yarda mu goyi bayan azzalumai. Mahaliccinmu Ya tabbatar da cewa in muka ki bin umurninSa, to, lallai azabar wuta za ta shafe mu tare da azzaluman da muka goyi bayansu.
Ya jama’a, mu kalli rayuwarmu ta yau, shin muna bin umurnin Allah kuwa? Kiri-kiri za ka ga mutum ya goyi bayan azzalumi ba don komai ba, sai don jam’iyyarsu daya ko yarensu daya, ko addinin su daya, ko garinsu daya, ko jiharsu daya, ko kasarsu daya, ko yanki daya suka fito. Shin wannan mummunar dabi’a za ka same ta a wurin mutumin kirki kuwa? Yau an wayi gari ba mu kyamar zalunci da azzalumai saboda kwadayin abin duniya da son zuciya.
Mu kalli yadda cin hanci da rashawa suka yi katutu a Najeriya, Allah Ya albarkaci wannan kasa da duk nau’o’in albarkatu, amma saboda zalunci da cin hanci da rashawa da rashin adalcin shugabanni, an wayi gari kasar tana neman rushewa. A yau kowane fanni ka duba za ka ga ba inda zalunci da cin hanci da rashawa ba su yi katutu ba. Bayan wannan, babban bala’in ma shi ne goyon bayan masu zaluncin don abin duniya, ko wata bukata ta kashin kai. Wannan ya jawo ba a gudun aikata zalunci, domin mutane sun san duk zaluncin da za su yi, duk satar da za su yi, matukar suna da abin hannu, ko kuma suna da daurin gindi, to al’umma za ta karbe su hannu bibiyu, a girmama su, a ba su sarautun gargajiya ko digirin girmamawa ko wani matsayi a cikin al’umma. Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!!!
Ku sani lallai idan aka wayi gari al’umma ta zama haka, to sai dai a ce Allah Ya kiyaye, kuma kashin ta ya bushe, kuma sai buzun ta. Domin tabbas Allah zai jarrabi wannan al’umma da abubuwa marasa dadi iri-iri, daban-daban, masu yawa, kamar yadda muke gani, muke ji, kuma muke dandanawa a yau.
Ya ku jama’ah! Lallai ku sani, lokaci ya yi da za mu dakatar da wannan mummunar dabi’a domin Allah Ya dube mu da idon rahama, Ya tausaya mana, Ya kawo muna karshen wadannan bala’o’i da suka addabe mu, musamman rashin tsaro, talauci, yunwa, matsalar tattalin arziki da sauransu.
Ya ku ‘yan uwa! Saboda munin zalunci fa Allah Yace lallai Ya haramta wa kanSa zalunci, kuma Ya sanya shi ya zama haramun a tsakaninmu, saboda haka ya ce, kada mu zalunci juna. Amma duk mun manta da umarnin Allah, an wayi gari muna goyon bayan azzalumi saboda dan uwana ne, ko addininmu daya, ko dan jami’yyata ce, ko yare na ne, ko don kwadayin abin hannunsa. Kuma da wannan mummunar dabi’a, wai mu ce mu Musulmin kwarai ne, ko muce mu mutanen kirki ne masu fatan samun rahamar Allah! Shin muna nufin za mu yaudari Allah ne? Ya kamata mu shiga taitayinmu domin wallahi Allah ba abin wasa ba ne.
Imam Ibnu Kasir a yayin da yake bayani game da ayar da ta yi hani a kan goyon bayan azzalumai da ke cikin Suratul Hud: 113, ya ce:
“Fadin Allah cewa, “Kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku.” Aliyu bin Dalha ya ruwaito daga dan Abbas cewa, ma’anarta: “Kada ku mika wuya ga azzalumai.”
Imam Al-Aufiy kuwa ya ruwaito daga Dan Abbas (RA), cewa: ma’anarta shine, “Kada ku karkata da goyon bayan shirka da zalunci.”
Kuma Abul-Aliyah ya ce, ma’anarta, “Kada ku yarda da aikin zalunci da ayyukan azzalumai.”
Shi kuwa Imam Ibnu Jarir ya ruwaito daga Dan Abbas (RA) cewa, ma’anarta: “Kada ku karkata ku goyi bayan azzalumai.”
Daga karshe Ibnu Kasir ya ce, zance mafi kyau game da fassarar ayar, shi ne; “Kada ku taimaki azzalumai a kan zaluncinsu, ta hanyar goyon bayansu. Domin duk wanda ya aikata haka, to ya yarda da aikinsu na zalunci ke nan.”
Lallai mu sani, wannan aya ta kai makura wajen hani a kan zalunci da goyon bayan azzaluman shugabanni. To idan Allah Ya yi tanadin azabar wuta ga wanda ya karkata zuwa ga azzalumai, to ina ga wanda ya yi dumu-dumu cikin goyon bayansu ta hanyar yi musu kamfen na siyasa da sauransu, don abin da zai samu a hannunsu ko domin wata maslaha ta kashin kan sa?
Lallai ko shakka babu, goyon bayan zalunci da azzalumai haramun ne, Allah Ya hana. Sannan yana daga cikin zunubai masu girma, (Wato Kaba’irai). Domin Allah Ya yi alkawarin narkon azaba a kan wannan. Sannan mu sani, abin da kawai ya halatta mu yi ga azzalumi, shine mu taimake shi mu hana shi yin zaluncin. Idan shugaba ne kuwa, mu hana shi ci gaba da shugabancin, mu haramta masa rike ko wane irin mukami har abada, ta hanyar da dokar kasa ta yi tanadi, (Wato kuri’un mu), ba ta hanyar fitina da tada hankali ba.
Imam Al-Zamakhshari ya ce:
“Hani a kan goyon bayan azzalumai ya hada da kada ka shiga cikin bin son zuciyarsu, ka nisance su, kada ka yi abokantaka da su, kada ka zauna da su, kada ka ziyarce su, kada ka yi shiru a kan zaluncin su, kada ka nuna amincewar ka a kan zaluncin su, kada ka yi kamanceceniya da su, kada ka kwaikwaye su ta kowace fuska, kada ka yi kwadayin abin hannun su, kada ka yabe su ka nuna cewa su masu girma ko mutunci ne, kada ka nemar musu jama’a da magoya baya (Wato yi masu kamfen).”
Kuma an ruwaito cewa: “Babban malami daga cikin magabata da ake kira Al-Muwaffik, wata rana yana Sallah a bayan wani limami, sai limamin ya karanta Suratul Hud, da ya kawo daidai aya ta 113 inda Allah ke maganar “Kada ku karkata ku goyin bayan azzalumai, idan kun yi haka wuta za ta shafe ku.” Sai Al-Muwaffik ya fadi a kasa magashiyyan ya suma, a lokacin da ya farfado sai aka tambaye shi, gafarta Malam me ya faru ne? Sai ya ce, “Wannan ayar tana nufin Allah zai azabtar da wanda ya goyi bayan azzalumi ne, to ina ga shi azzalumin kansa?” Sai ya ce wannan shine na tuna dashi sai ya tsoratar da ni, hankali na ya tashi yasa na suma.”
Saboda haka ya ku ’yan Najeriya! Mu ji tsoron Allah, kuma mu sani, wallahi ba za mu kawo karshen zalunci ba, har sai mun daina goyon bayan mulkin azzalumai da mulkin danniya. Sai mun kyamace su da abin da suka mallaka. Amma muddin azzalumi zai yi zalunci ya tara abin duniya ta hanyar zalunci, kuma mu je muna kwadayin wannan abin nasa, muna girmama shi saboda abin duniya, to ba yadda za a yi zalunci ya kare a cikin al’umma.
Ya ku ’yan Najeriya! Lallai zaben 2019 yana isowa, ga mai yawancin rai daga cikin mu. Wannan lokaci ne mai matukar muhimmanci da tsada ga rayuwar mu, lokaci ne mai tsadar gaske, kar muyi sakaci da shi. Wane irin shiri da tanadi muka yi domin sa? Shin mun san muhimmanci da kyakkyawan tasirin zaben shugabanni na kwarai masu tausayi ga rayuwarmu kuwa? Shin za mu sake yarda da duk wani mayaudari da tun da aka zabe shi babu abinda ya tsinana muna illa azabtar wa? Ko za mu ci gaba da jefa rayuwarmu da ta ’ya’yanmu da jikokinmu cikin hadari ne? Shin har yanzu bacci muke yi ne ko mun farka daga dogon baccin mu? Shin za mu yarda mu ci gaba da rayuwa cikin kaskanci, wulakanci, yunwa, talauci, kuncin rayuwa da sauransu? Shin za mu yarda mu ci gaba da rayuwa irin ta bayi, duk shekara ana yin kasafin kudi (Budget), muna jin labarin tiriliyon na iska, na takarda kawai, amma ba su da wani tasiri da amfani ga rayuwar talakawa? Duk amsoshin wadannan tambayoyin da sauransu za mu fahimce su ne a zaben 2019, in Allah Ya sa muna raye. Kuma idan kunne ya ji, to gangar jiki ya tsira!
‘Yan uwa! Mu duba yadda tsananin yunwa da fatara da talauci da cututtuka da rashin tsaro da rashin hanyoyi masu kyau da rashin kyakkyawan ruwan sha da rashin magani a asibiti da rashin ingantattun makarantu, yara ba karatu, marasa lafiya ba magani, addini ba kulawa, marayu da gajiyayyu an yasar da su, duk da irin dimbin arziki da masu arziki da Allah Ya hore wa kasar nan. Wai a cikin irin wannan hali da yanayi ne kuma ake so mu yi fatar tabbatuwar wannan irin bakin mulki, mulkin da babu kwarewa ba tausayi da imani a cikinsa?
Ya ku Jama’a! Lallai ya zama wajibi a kan duk wani dan Najeriya ya yi wani abu domin samun canjin shugabanci nagari a wannan kasa. Dole ne mu canza wannan bakin canjin marar amfani, tunda canjin bai tsinana muna komai ba sai wahala. Ya zama dole mu zabi shugaba adali, mai kishin kasa, mai son ’yan kasa, mai kokarin hada kan ’yan kasa, jarumi, gwarzo, mara tsoro, mai tausayi, wanda ya fahimci kasar nan, wanda za ya bai wa kowa hakkinsa ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Dole ne mu zabi shugaba mai hankali, mai cika alkawari, mai daukar shawara, mai sauraron bukatu da matsalolin ’yan kasarsa. Dole ne mu zabi shugaba wanda zai kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasar sa, shugaba wanda zai ba kowa hakki da ’yancin yin addininsa ba tare da tsangwama ko nuna bambanci ba. Shugaba wanda zai yi kokarin wadata ’yan kasa da kayayyakin inganta rayuwa da kayan masarufi, shugaban da zai yi kokarin hana satar dukiyar al’umma, ya hana cin hanci da rashawa da gaske ba tare da nuna banbancin siyasa ba ko wani son rai, yaki da cin hanci da rashawan da za’a yi tsakani da Allah, ba wanda za’a tsangwami wasu ba wasu kuwa su zama shafaffu da mai. Shugaba wanda yake mai gaskiya, ba makaryaci ba, shugaba mai bin doka, ba mai kama-karya ba. Shugaba wanda ya fahimci cewa kasa da arzikin kasar na kowa da kowa ne ba na wani yanki kawai ba, kuma ya watsa arzikin domin amfanin al’umma, ba ya rike ya takura, ya hana ba.
Ya ku ’yan Najeriya! Lallai ku sani, irin wannan shugaban ba zai taba samuwa haka nan kawai ba tare da mun tabuka komai ba. Sai dukkanin mu mun a je son zuciyar mu, mun yi aiki da hankali da tunani da wayo da basirar da Allah Ya yi mana. Sai mun manta da duk wani soki-burutsu, yaudara, farfagandar karya, shirme da sauransu, mu kalli cancanta da dacewa kawai, musamman lura da halin da muke ciki a yau.
Idan kuwa mun ki ji, mun bi soye-soyen zukatan mu, to, ba za mu ki gani ba kuwa.
Allah ba ruwanSa, Ya riga Ya ba mu dama, Ya kuma ba mu zabi, idan har muka yi amfani da damar ta hanyar da ta dace, to mune za mu amfana, idan kuma muka banzatar da damar, to za mu ci gaba da shan wahala. Allah ba zai sauko Ya zabar mana shugabanni na kwarai masu tausayin mu ba, mu ne za mu yi da kan mu, don haka ya rage namu.
Ya kai dan uwa mai albarka! Ka sani, wallahi lokacin zaunawa ka rungume hannu ka ce kai babu ruwanka da sha’anin siyasa da sha’anin shugabanci a Najeriya ya wuce, domin idan bala’o’i suna faruwa a kasa sanadiyyar rashin shugabanci nagari, ba ka isa ka ce babu ruwanka ba, domin sai ya shafe ka ko ya shafi wani naka. Sannan ka mutu ka hadu da Allah Ya tambaye ka, me yasa ba ka bada gudunmawa domin tabbatar da shugabanci nagari a bayan kasa ba? Ka ga sai ka shirya irin amsar da za ka bai wa Allah Mahaliccin ka. Na yi imani, ko kai Musulmi ne ko Kirista, ko marar addini, dan Kudu ne kai ko dan Arewa, lallai na san kana ji a jikinka a wannan mulkin.
Ya ’yan uwa! Wallahi ba mu da wata hujja da za mu kare kanmu da ita a gaban Allah gobe kiyama, a kan mun san cewa mutum baya da koshin lafiyar da zaya iya gudanar da mulki, kuma mun san ba ya da kwarewa ko wayewa da sanin ya kamatan da zai shugabanci kasa ko al’umma, amma mu dage muce dole sai mun goyi bayansa ya ci zabe. Mu zabe shi ko mu ba shi kuri’armu don kawai kare maslahar kashin kanmu. Lallai mu sani, wallahi yin haka zai jawo mana matsala tun a nan duniya kafin mu je Lahira. Saboda haka ya zama dole mu yi karatun ta natsu, mu canja tunanin mu, sannan mu ji tsoron Allah.
Allah ya sani, kuma shi shaida ne, kuma jama’a ma shaida ne. Mun yi wa wadannan shugabanni kyakkyawan zato na alkhairi, cewa da ikon Allah idan sun zo za su iya gyara kasar nan, za su iya samar da canjin da muka jima muna nema ido rufe. Mun nuna masu so da kauna, mun yi masu Kamfen, mun zabe su. Sun dau alkawurra cewa za su kauda muna da matsalolin da ke damun mu da damuwowin da suka addabe mu, muka zabe su, muka basu kuri’unmu, muka bata lokutan mu masu tsada, wasun mu sun rasa rayuka wajen zaben nan, wasun mu sun rasa hannu, wasu sun rasa kafa, wasu sun rasa dukiyoyin su. Sai bayan kun hau mulki da shekaru biyu da rabi, sai muka ga sabanin haka, sai gashi yanzu abubuwa suna faruwa marasa kyawo, marasa dadi a gwamnatocin ku, kuna kokarin gaya muna ai kaddarar Allah ce! Haba wace irin kaddara? Kaddara ko dai sakacin ku? Kaddara ko dai rashin iya mulkin ku? Muji tsoron Allah mana ‘yan uwa kuma mu gyara!!!
Allah fa babu ruwan sa, idan kayi mai kyau kuma ka nemi agajin sa, za ya taimake ka kuma ya agaza maka a kan mulkin ka. Idan kuwa ka ki ji, ka ki daukar shawara, ka raina bayin sa, ka dauke su ba bakin komai ba, kana ganin kai kadai ne ka iya, sai ya zare hannun sa a harkar mulkin ka da dukkanin al’amurran ka, a wayi gari abubuwa sun rikice maka, su cakude, ka rude, ka rasa yadda za ka yi. Talakawa kuma suyi ta Allah waddai da bakin mulkin ka, saboda masifar da suke ji a jikinsu.
Mu ji tsoron Allah ya ku ’yan Najeriya! Muji tsoron Allah ya ku muninai! Mu nemi kusancin Mahaliccinmu ya ku bayin Allah! Da tabattuwa a kan gaskiya komai dacin ta, da yakar zalunci da azzalumai, mu tuba zuwa ga Allah baki daya, ko ma rabauta.
Ya Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka taimaki Najeriya da ’yan Najeriya, Ka kaskantar da kafirci da kafirai, Ka halakar da makiyanka makiya addininKa, wadanda ba sa son a zauna lafiya a Najeriya da duniya baki daya. Ka taimaki bayinKa salihai a duk inda suke, ka rusa ta’addanci da ‘yan ta’adda, Ka ba mu ilimi mai amfani. Kuma Ka nuna mana gaskiya Ka ba mu ikon bin ta, Ka nuna mana karya, ka ba mu ikon guje mata.
Ya Allah ’yan uwanmu mutanen jihohin Borno, Yobe, Adamawa Zamfara da sauran jihohi da garuruwa, da Ka jarabce su da fitintinu da tashe-tashen hankula daban-daban, Ka kawo masu saukin wannan wahala. Ya Allah Ka jikansu, Ka tausaya masu Ka sa duk wannan wahala ta zama kaffara a gare su. Ya Allah Ka albarkace su da mu baki daya da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ka wadata kasarmu Ka zaunar da mu lafiya. Ya Allah kayi muna maganin satar mutane domin samun kudin fansa (Wato Kidnapping) a kasar nan, amin.
Ina fadar wannan magana tawa ina neman gafarar Allah a gare ni da ku da dukkanin Musulmi daga dukkan zunubi da kuskure, ku nemi gafararSa lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.
Imam Murtadha Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Unguwar Nagazi-Uvete, Okene, Jihar Kogi Najeriya. Za’a iya tuntubarsa ta: +2348038289761 ko kuma gusaumurtada@gmail.com