Shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomi shida cikin bakwai na Kaduna ta tsakiya sun amince mai ba gwamnan Kaduna Shawara kan harkar siyasa, Uba Sani ya fito ya tsaya takaran kujeran sanata na Kaduna ta tsakiya a 2019.
Shugabannin sun sanar da haka ne bayan wata ganawa ta musamman da suka yi a Kaduna ranar Asabar.
Shugaban Jam’iyyar APC na Kaduna ta Arewa, Musa Sheriff wanda shine ya karanta matsayar su ya ce ganin irin abubuwan da Uba yayi wa matasa musamman a yankin Kaduna ta tsakiya da ya hada sa samar musu da ayyukan yi da sauran su ya sa suka yanke shawaran kira gareshi da ya fito yayi takaran kujeran Sanata na Kaduna ta tsakiya a zaben 2019.
Shugabannin jam’iyyar da suka sa hannu a takardan sun hada da na Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Chikun, Birnin Gwari, Kajuru, da Giwa.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Kaduna ta Arewa, a wani shirin radiyo a Kaduna sunce shugabannnin sun ari bakin su ne sun ci musu albasa.
Sun ce ba su da masaniya kan abin da shugabannin su ka fadi cewa babu ruwan su kuma su ba sa tare da su.
Sanata Shehu Sani ne ke wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar Kasa.