A kasar nan an rigaya an cusa kiyayya ga Fulani makiyaya a kafafen yada labarai.
Idan za a bi dare ana kashe Fulani, to mafiyawa daga cikin jaridun Kasar nan ba za su dauki abin har su yayata shi ba yadda ya kamata.
Ko da ko kisan kare dangi ne akayi wa wadannan Fulani.
Sai ranar da Fulani suka gaji da jiran hukuma ta yi wani abu, idan ba ta yi ba, sai suka bi dare su dauki fansa, to ranar ne duk jaridu da kafafen yada labaran kasar nan za su cika jama’a da labaran Fulani sun yi kisa.
Kai wadanda ba aiki jaridar suke yi ba, za su fito a lokacin suna kokarin baza hazakar zubutun su domin nuna kiyayyar su karara ga Makiyaya.
Game-garin mutanen da ba a sanar irin barnar da aka yi wa Fulani kafin su dauki fansa ba, sai su rika kara cusa wa kan su da ’ya’yan su kiyayya da tsanar Fulani.
An karkashe Fulani makiyaya da daruruwan dabbobi da yawa a kasar nan. Duk wannan kisan da aka yi musu bai girgiza marubuta da ’yan katsalandan din kisan kabilar da aka raunana ba, musamman kisan da Fulani su ka yi a Benuwai na kwana-kwanan nan.
Ya kamata gidajen jaridu su sani cewa, idan za a shekara 100 suna danne kisan da ake yi wa Fulani ba su bayyanawa, to ai su Fulanin sun san cewa an kashe su.
Sau da dama fadace-fadacen nan na ramuwar-gayyar daukar fansan kisan da aka yi ne baya, shekaru daya, biyu, uku kai ko ma biyar baya.
Sau da yawa saboda kokarin dankwafar da Fulani da kuma rufe barnar da ake musu, sun daina ganin Fulani a matsayin wasu mutane sahihai. Haka kuma ba su dauki shanu da daraja ba.
Idan aka kashe wa Bafulatani shanu 15, wadanda kudin su ya kai naira milyan biyu da rabi, to jaridu ba za su dauki labarin da muhimmanci ba.
Sai ranar da Fulani su ka bi dare suka kone bukkoki biyar wadanda bukka daya tal za a iya gina ta da naira dubu 20,000, to sannan ne aka samu labarin bugawa ana yayatawa duk duniya ta sani.
Dole gidajen jaridun kasarnan su mai da hankali wajen nuna kwarewa a aikin su, sannan su dinga bada rahoton abinda yake faruwa ba tare da suna zabin wanda suka fi so su yayada ba.
Idan ba a manta ba, kauyuka kusan 4 ne aka shafe su a karamar hukumar Numan, jihar Adamawa a kwanakin baya. Dukiyoyi, yara da mata, an sace shanu sama da 500 sannan an kashe dayawa. Amma ji kake kamar ba mutane ne su ba.
Haka ma ba za ayi saurin manta abin da ya faru a tsibirin Mambila ba. Duk basu zama abin damuwa da abin ruruta wa ba domin a dauki mataki akai ba.
Wani Janar din sojin Najeriya ya fito fili karara a lokacin ya bayyana cewa bai taba ganin kisan kare dangi ba a tsawon aikin sa na soja irin abin da ya gani anyi wa Fulani mazauna tsibirin Mambila din.
Yanzu dai gashi an bankado wata sabuwa inda aka gano wasu boyayyun daruruwan matasa da makamai mallakar gwamnatin Benuwai da sunan wai masu kare mutane.
Dole ne jaridun Kasar nan su gyara aikin su wajen fadin gaskiya da tsara labaran su cikin kwarewa da fede gaskiya daga kai har bindi.
Discussion about this post