Shekarun balagar mace ko Namiji ya yi matukar raguwa – Binciken Kimiyya

0

Wasu masu binciken kimiya a Melbourne kasar Australia sun gano cewa yawan shekarun da kan dauki ‘ya mace ko namiji ya ko ta balaga yayi matukar raguwa yanzu.

Binciken ya nuna cewa ba kamar da ba da ‘ya mace bata balaga sai ta kai shekaru 12 ko kuma 13 yanzu ya nuna cewa yarinya kan balaga tun daga shekara 9 zuwa 14 sannan namiji daga shekara 10 zuwa 16.

Bisa ga wannan bayanai da aka gano yanzu, masu binciken sun yi kira ga gwamnatocin kasashe da su gyara dokokin kasar su na shekarun da balagagge ke da ‘yancin yin wasu abubuwa a matsayinsa na cikakken mutum.

Share.

game da Author