SHAWARA: Za a fara yin rigakafin cutar a Jihohi Kogi, Kwara, Zamfara da Barno

0

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko Faisal Shuaib ya ce gwamnatin tarayya tare da hadin guiwar kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO sun fara bada alluran rigakafin cutar shawara wato ‘Yellow Fever’ a jihohi uku na kasar nan.

Jihohin da aka fara bada wannan alluran sun hada da Kogi, Kwara da Zamfara sannan bayan haka za a ci gaba har zuwa jihar Barno.

“Muna sa ran cewa mutane miliyan 8.6 a wadannan jihohi 4 ne za a yi wa allurar.”

Shuaib wanda ya sanar da haka a yau Alhamis ya ce wannan dabara ce da suka dauka domin kawar da cutar nan da shekaran 2026.

Ya kuma kara da cewa kungiyar WHO ta yi alkawarin samar da rigakafin cuta miliyan 20 duk shekara har na tsawon shekaru tara sannan za ta tallafa musu don ganin an sami nasara a wannan abu da aka sa a gaba.

Share.

game da Author