Shan magani ba tare da umarnin likita ba kan sa ya ki aiki a jiki

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya na duniya ‘WHO’ ta ce binciken da ta gudanar ya nuna mata cewa maganin dake kara karfin garkuwar jikin mutum wato ‘Anti-biotics basu warkar da cutukan da ya kamata.

Jami’in kungiyar Marc Sprenger yace ana samun haka ne idan mutane na yawan amfani da maganin ta hanyoyin da bai kamata ba wanda hakan ke samar wa cutuka damar Zama a jikin mutum.

Ya bayyana cewa cututtuka kamar su cutar sanyi , cutar hakarkari (Pneumonia), ciwon ciki da ake kira ‘Salmonella spp’ na cikin cutukan da basu jin wannan magani.

Ya ce binciken ya nuna cewa wannan matsalar ana fama da shine a duk kasashen duniya.

Share.

game da Author