Sarkin Musulmi da Oni na Ife sun nemi a kafa kwamitin da zai binciki kashe-kashe a Najeriya

0

Majalaisar Sarakunan Gargajiya ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo karshen mummunan kashe-kashen da ake tabkawa a kasar nan, ta na mai nuni da cewa ran dan adam ya na da darajar da bai kamata ana zubar da jinin sa ba.

Shugaban Majalisar ne, kuma Sultan na Sakkwato, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana haka a garin Fatakwal ranar Talata.

Sa’ad Abubkar ya kuma yi kiran da a kafa kwakkwaran kwamitin bincike wanda zai binciki kashe-kashen da ake yawan yi a fadin kasar nan.

Sultan ya kuma roki gwamnati da jami’an tsaro su tashi haikan su magance kalubalen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Ya kamata mu yi tunanin cewa tun cikin 1914 mu ke tare a matsayin kasa daya, don haka babu daren da jemage mai bani ba. Yanzu mun zama daya, ba kamar masu rike da mukaman siyasar da ke da adadin lokacin karewar zangon mulkin su ba.” Inji Sultan.

Shi ma Oni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, ya ce tilas ne sarakunan gargajiya su cire son rai da ra’ayin siyasa su taimaka wajen shawo kan kalubalen da ke tunkarar kasar nan.

Share.

game da Author