Jiya Litinin ne ’Yan Kwamitin Majalisar Dattawa a Harkokin Kwastan, su ka sake rukumewa tsakanin su da Hameed Ali, Shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa.
Wannan sabon sabanin ya afku ne yayin da mambobin kwamitin kwastan kan kayan da ake lalatawa, karkashin shugaban su, Sanata Dino Melaye suka yi wa shugaban na kwastan korafin cewa bai sauko ya tarbe su ba, a lokacin da suka kai masu ziyara. Maimakon haka, sai ya zarce dakin taro kawai.
Dino Melaye ya ce a bisa tsari ko al’ada ta Majalisar Dattawa, idan muka kai wa shugabannin kwastan ko na jami’an shige da fice ziyara, to shugaban su kan sauko ya tarbe su da lale marhabin.
A bisa dukkan alamu wannan kalami bai yi wa Shugaban Kwastan dadi ba, musamman ganin yadda Dino ya yi masa magana haka gatsal a gaban mukarraban sa.
Hakan ne ya sa shi kuma ya maida musu kakkausar amsa, mai zafi. Ga dai yadda tankiyar ta kasance.
TSAURIN IDON:
“To kafin na fara karanta bayani na, bari na dan yi tsokaci dangane da yadda shugaban hukumar kwastan ta kasa ya karya doka ko ya saba al’adar da ake a kan ta dangane da tsarin zuwan kwamitin majalisa a nan hedikwatar kwastan.”
“Wato maimakon Shugaban Kwastan ya tsaya a kasa ya tarbe mu idan muka shigo, kamar yadda ake yi a ko da yaushe shekara da shekaru, sai kawai shi da mukarraban sa suka hau sama suka iske mu mu na jiran su.”
Nan da nan shi kuma Shugaban Kwastan, sai ya amayar da abin da ke cikin zuciyar sa nan take:
KAKKAUSAN RADDIN SHUGABAN KWASTAN:
“To mu ma mu na da irin na mu tsarin na hukumar kwastan da ya danganci karbar baki irin ka. Ni ba na bukatar na sauko kasa na tarbe ka, kamar yadda babu wani Sanata ko Dan Majalisar Tarayyar da ya taba sakkowa ya tarbe mu a duk lokacin da mu ka ziyarci Majalisar Tarayya.”
“Bari dai na sake fitowa karara na shaida maka cewa mu a Hukumar Kwastan ta Kasa, dukkan mu jama’a mu ke wa aiki, kuma mun yi amanna da Najeriya. Shi ya sa mu ke aiki ka’in da na’in domin mu kara ciyar da kasar mu gaba. Don haka shi ya sa mu ke aikinmu, ba mu yarda wani dan katsagalli ya yi mana katsalandan.”
Idan dai ba a manta ba, sun fara samaun takun-saka ne tun cikin watan Mayu, 2017, lokacin da suka ce tilas a matsayin san a Shugaban Kwastan, sai ya sa kakin su.
Shi kuma ya kekasa kasa ya ce babu wanda zai tilasata masa dauka kakin kwastan, tunda dokar kasa ba ta ce sai ta daura ba.