Sama da mutane 25,000 ba sa karban fansho a kasar nan

0

Shugaban kungiyar ‘yan fansho na Najeriya ‘NUP’ Joseph Dele ya ce sama da mutane 25,000 na ‘yan fansho basa karban kudaden fasho a kasar nan.

Ya fadi haka ne da yake hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya ranar Lahadi inda ya kara da cewa wadannan mutane basu cikin 300,000 dake karbar Fansho a yanzu.

Dele ya kuma karyata zargin da Atone-Janar na kasa Abubakar Malami ya yi cewa da hadin bakin kungiyar ‘NUP’,aka salwantar da kudaden ‘yan fansho a baya.

” Gaskiyar magana shine ‘yan fansho 25,000 din nan ba na boge bane sannan ba a basu hakkunan su wato kudaden su na fansho.”

Daga karshe ya ce kashi daya bisa 100 ne kacal NUP take samu daga cikin kudaden ‘yan fansho duk wata domin ta kula da harkokin kungiyar na yau da kullun.

Share.

game da Author