Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sai da yayi ‘yar gajeruwar suma lokacin da tsohon shugaba kasa Goodluck Jonathan ya kira ranar da aka sanar da sakamaon zaben shugaban kasa yana taya sa murnar lashe zaben.
” Ba zan taba mantawa da wannan rana ba da kuma wannan lokaci da ya kirani. Ya kirani da karfe 5 da kwata daidai.”
” Jonatahan ya dade a karagar mulki tun daga mataimakin shugaban kasa zuwa har ya shugabanci kasar nan na tsawon shekara shida zai iya dabutarta komai alokacin amma baiyi haka ba, ya hakura ya rungumi wannan sakamako.
Buhari ya ce hakan ba karamin jarumtaka bane.