Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar cewa ta kammala shiri tsaf domin mika wa sabbin malaman firamare da zata dauka takardun samun aiki da jihar.
Wadanda aka dauka za su fara aiki ne a watan Fabrairu sannan ma’aikata ne na dindindin kuma za mu sa su cikin shirin fansho.
Gwamna Nasir El-Rufai ya sanar da haka ne da ya ke ganawa da shugabannin kananan hukumomin jihar da sakatarorin ilimi na kananan hukumomin.
A ganawar shugabannin kananan hukumomin sun koka kan yadda kungiyar ‘yan kungiyar malamai na NUT ke muzguna wa malaman dake zuwa aiki don bin umarnin gwamnatin jihar.
El-Rufai ya ce har yanzu kofar gwamnati a bude yake cewa duk wanda yake so ya yi aikin malunta a jihar zai iya mika takardun sa a hukumar SUBEB na jihar.
Bayan haka ya gargadi masu zuwa domin korar malaman da suke zuwa aiki cewa, wannan ba hurumin su bane. Ma’aikata dai na gwamnati ne su iya nasu suyi zanga-zanga, kuma sun yi.