RIKICIN MAKIYAYA DA MANOMA: Osinbajo zai shugabanci kwamitin gwamnoni tara don magance kashe-kashe

0

Majalisar zartaswa na Kasar nan, NEC, ta kafa kwamitin gwamnoni tara da za su shawo kan rikicin Fulani makiyaya da manoma. Kwamitin na karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Gwamnan Jihar Kano, Adulllahi Ganduje ne ya bayyana haka bayan fitowar su taro, a Abuja, inda ya ce sauran ‘yan kwamitin sun hada da gwamnonin Zamfara, Kaduna, Adamawa, Benue, Taraba, Edo, Plateau, Ebonyi da kuma Oyo.

Ganduje ya ce tuni kwamitin ya fara zaman tautauna abubuwan da ke gaban sa. Ya kuma kara da cewa kwamitin zai yi aiki ne tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk masu hannu a cikin rikice-rikicen.

Share.

game da Author