Rashin murza tamola a Leicester yasa Ahmed Musa ya koma in da ya fito, CSKA Moscow

0

Kungiyar Kwallon Kafa ta CSKA Moscow, ta bayyana cewa dan wasan Super Eagles na Najeriya, Ahmed Musa, ya sa hannun komawa kungiyar daga Leichester City da ke Ingila.

Tuni har kungiyar ta ce za a saka sunan dan wasan a cikin jerin wadanda za su fafata a gasar cin Kofin Kalubale na Turai, Europa da za a fara wasan siri-daya-kwala, nan ba da dadewa ba.

Kafin sannan dama Rohr, mai horas da wasan Super Eagles, ya bayyana yiwuwar komawar Ahmed Musa CSKA Moscow, wanda ya ce hakan wani karin kwarin gwuiwa ne ga dan wasan da kuma Super Eagles baki daya.

Ahmed dama ya koma Leichester ne cikin 2016 daga kungiyar ta CSKA. Sai dai tun bayan komawar tasa, bai yi wani abin a zo a gani sosai ba. Hakan ya sa an rika ajiye shi a benci, wanda hakan na nuni da cewa idan ya ci gaba a haka, to da wahalar gaske a tafi gasar cin Kofin Duniya da shi.

Share.

game da Author