RAHOTO: Yadda mu ka zama bayin karfi da yaji a Libiya

0

Wasu ‘yan Najeriya da suka kubuta kuma suka dawo gida, sun bayyana yadda aka sayar da su, su ka koma yin bautar karfi da yaji a matsayin bayi a kasar Libiya.

Faith Oboh, mai shekaru 22, ta na daga cikin wasu da suka dawo daga Libiya su sama da 200 da ke karkashin kulawar gwamnatin jihar Edo.

Wakilin mu ya ci karo da ita a hukumar da ke tattara bayanan gudaddun wadanda aka bautar a kasar Libiya da ake tantancewa a jihar Edo.

Kai da ganin Oboh, ka san cewa a firgice ta ke, kuma ta fita daga kamannun ta. Ta na mu’amala da jama’a ba a cikin sakin jiki ba, tamkar ‘yar da iyayen ta su ka tsine wa, kuma suka kore ta daga gida.
Amma fa ita ce ta uku daga cikin ‘ya’yan da mahaifin su ya haifa su 12.

Da ta ke bada labarin irin bautar da ta yi, Faith ta tuna da cewa kafin ta bar Najeriya, da ita sama’ar kitso da gyaran gashi take yi. Amma tsananin talauci ya ingiza ta neman abin duniya, ta hanyar shiga Saharar kasar Libiya.

“Haka na kwashi dan abin da na ke adanawa daga kudin kitson da na ke samu a nan Najeriya, na biya tsabar kudi har naira 500,000 ga wani wanda ya gabatar min da kan sa cewa shi ne mai safara da jigilar mutane zuwa Libiya.

“Amma ni dama muradi na shi ne daga Libya, na shiga jirgin ruwa na tsallaka teku zuwa Italy. Amma sai wani al’amari ya auku. Injin jirgin ruwan da mu ka shiga daga Libya, sai ya samu matsala, bayan mun kai tsakiyar ruwan tekun Medditerranean. Sai da muka yi awa 12 ba gaba, ba baya.

“A nan fa maza da mata har da kanan yaran da mu ke cikin jirgin, kowa ya dukufa sheka ruwan addu’o’i ba kakkautawa. Ga kuka mu na yi, ga kuma igiyar ruwa sai kara murda jirgin mu ta ke yi da karfi. Al’amarin ya dagule mana, ganin cewa direban jirgin ya kira lambar wayar ‘yan sandan Libya, domin su zo su cece mu.

“A karshe, bayan an kubutar da mu, sai aka tsare mu a wani sansani a Libiya, inda muka rika fuskantar muzgunawa da kaskanci da kunci da takaici, har tsawon shekara daya cur.

“Maganar da na ke yi maka a yanzu ban san inda aka milla da wanda ke mana jagorar tafiyar mu ba. Ban ma sani ba, ta na dai rai, ko ta mutu.” Inji Faith.

Ita ma wata mai suna Blessing Braimah, mai shekaru 34, kuma mai ‘ya’ya hudu, ta bayyana cewa kaddara da neman duniya ya kai ta ga afkawa cikin halin kunci da kangin bauta a Libiya, domin ta fice daga Najeriya ne, a lokacin da ta ke kan ganiyar samun nasibin kasuwancin da ta ke yi.

Ta ce a haka kawai ta tsallake ta bar ‘ya’yan ta, kuma ta bar sana’ar da ta ke yi aka yi mata romon-kunne cewa ta na zuwa Turai za ta kudance.

Blessing ta ce haka ta kwashi dan jarin ta, har ma ta hada da ramtar naira 600,000, ta nausa Libiya, da nufin daga can ta zarce Turai, ta samo kudin huce takaicin rayuwa ita da iyalin ta.

Sai dai kuma ta kara da cewa ta fara samun matsalar sana’ar da ta ke yi a Najeriya ne, bayan da mijin ta ya tsallake, ya gudu ya bar ta da ‘ya’ya hudu da ta ke daukar nauyin ciyar da su, ita kadai.

Ta ce to daga nan ne ita kuma ta fara tunanin tafiya Turai, inda a karshe ta tsinci kanta a Libiya.

“Mun ga bala’i, mun sha wahala da wulakanci a Libiya, saboda kasar ko kuma inda muke ya kasance tamkar filin yaki, inda ba za ka iya sanin abin da zai faru da kai nan da minti daya ba.” Inji ta.

Ta ce an kulle su a cikin kurkukun Tripoli, ita da wasu da dama. Ta na mai cewa dama tun a cikin Sahara ma su ka fara yin arba da bala’i kuru-kuru, domin ta ko’ina sai su rika jin karar zabarin bindigogi kawai – ratatatatatata!

“Tuni na so dawowa Najeriya,ba sai yanzu da aka kwaso mu ba. To amma fa ka san ba tafiya ba ce da kawai zaka je tashar mota ka nemi motar Najeriya, ka hau a kawo ka gida ba.’’

Blessing ta ce inda ake kara cin wata tsananin bakar wahala sai cikin sansanin da su ke killace jama’a.

Shi ma wani da aka dawo da shi kwanan nan mai suna Osaze Imafidon, rayuwar sa ba za ta taba komawa kamar yadda ya ke kafin ya tafi Libiya ba, domin a can ya zama nakasasshe, ba ya iya tafiya sai ya na dogara sanduna guda biyu, daya a kowane hannun sa.

Imafidon ya ce harbin sa aka yi da bindiga a kafa daya, haka kawai don gadara, har sai da ta kai an guntule masa kafar.

“An harbe ni ba don na yi wani laifi ba. Su kawai harba bindiga a kasar ya zama kamar wasan kwallo ne. Haka kawai sai dai ka ji an bude wuta ta ko’ina ta-tas ta-tas ta-tas, tas, tas, tas! Ga shi kuma kowa rataye da bindiga kamar yadda mu ke rataya sarka a nan.”

“su fa rayuwar bakar fata ba a bakin komai ta ke wurin su ba. Sai a shigo har cikin dakin ka, a dauke duk wani abu da ka ke da shi mai daraja ko mai tsada, idan kuma ka yi magana, sai a dirka maka bindiga daram!”

Wakilin gwamnatin jihar Edo mai kula da wadanda aka dawo da su daga Libiya, ya shaida wa wakilin mu cewa irin labarin da ake zuwa musu da shi daga Libiya, abin firgici ne matuka.

Ya ce kuma su na ci gaba da wayar wa matasa kai da yi musu nasiha cewa kasashen Turai fa ba yadda ake ba su labari su ke ba. Don haka su rika hakuri da Najeriya.

Share.

game da Author