PDP ta fara laluben dan takarar shugaban kasa a 2019

0

Shugaban Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP,Walid Jibrin, ya bayyana cewa jam’iyyar su ta fara laluben wanda za ta tsayar a matsayin dan takarar ta na zaben shugaban kasa a zaben 2019.

Jibrin ya kuma jaddada fatan da su ke da shi cewa wasu ‘yan jam’iyyar da a yanzu ke cikin APC, za su dawo gida cikin jam’iyyar su ta asali, PDP.

Jibrin ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke karbar bakuncin wata ziyara da kungiyar wakilan mazabu da su ka kai ziyar a ofishin sa da Legacy Plaza, Abuja.

Ya kara da cewa wadanda su ka fice daga PDP a cikin 2015, duk za su dawo gida cikin PDP nan ba da dadewa ba.

Bayan ya jinjina kuma ya yabi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, inda ya ce mutumin kirki ne, sai kuma maida hankali wajen Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, tsohon gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso, Aminu Tambuwal da sauran wasu ma duk ya ce za su koma PDP.

“Ba mu da wani sabo ko kwantaccen rikici a PDP, saboda dukkanin mu mun amince cewa daga Arewa ne PDP za ta tsaida dan takarar shugaban kasa na zaben 2019. Don haka ina rokon da ku mara wa dan takarar Arewa din nan baya domin ku samu shugabancin da ya cancanta.

“ Mu na kuma yin dukkan iyakar kokarin mu domin ganin daga Arewa din mun tsaida dan takarar da ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya, wanda zai iya kwace mulki daga jam’iyya mai mulki. Saboda shekarar 2019 ta mu ce.

Share.

game da Author