NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSSCE ta Nuwamba/Disamba 2017

0

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa, NECO, ta bayyana sakamakon jarabawar SSSCE da aka zauna a cikin watannin Nuwamba da Disamba, 2017.

‎Shugaban hukumar ne, Charles Uwakwe ya bayyana sakamakon a Minna. Ya ce dalibai 42,985 ne su ka yi rajista, amma 42,429 ne suka rubuta jarabawar a darussa har 28.

Ya kara da cewa dalibai 24,098 ne su ka samu kiredit 5 zuwa sama, yayin da aka kama 4,425 da laifin satar jarabawa.

Uwakwe ya kara da cewa an samu raguwar masu satar jarabawa da kashi 5 bisa 100 idan aka kwatanta da 2016.

Ya ce an fito da smakamakon da wuri ne domin dalibai su samu damar shiga jami’a kan lokaci a wannan shekarar.

Wannan ne karo na farko ta tarihin jarabawar da aka fito da sakamako kwanaki 38 kacal bayan rubuta jarabawar.

Share.

game da Author