NAZARI NA MUSAMMAN: Rincabewar Fadan Makiyaya da Manoma a Arewa ta Tsakiya

0

Fulani makiyaya, mutane ne da a rayuwa ba su sa komai a gaba ba, in banda kiwon dabbobin su, wadanda akasari sun hada da tumaki, shanu da awaki. Kalilan daga cikin su da ke zaune a wuri daya, su kan hada da kiwon kaji da zabbi.

Fulani makiyaya ba su gaji zama wuri daya ba, kuma ba wai don wurin ne bai yi musu ba, sai kawai don matsawa gaba a nemi inda yalwar abincin da za su ciyar da dabbobin su ya ke. Komai nisan wuri idan dai akwai albarkar ciyawa da sauran ganyayen da dabbobi ke ci, to wurin bai yi wa Bafulatani nisa ba.

Duk ta yadda za ka bayyana Bafulatanin daji makiyayi, za ka taras matsolo ne, wanda ko kadan ba ya son yin amfani da dukiyar da ya tara domin ya biya wata bukata ta jin dadin rayuwar sa. Ko a gida ko a tsakiyar dokar jeji, da wuya ka ga sun bugi gaba sun yanka tuntiya, rago ko akuya don kawai su ci nama ba, ko da kuwa sun a da daruruwan dabbobi a tattare da su. Idan ka ga sun yanka akuya ko kaza sun ci, to ta kasa ne, aka yi a-kawo-wuka, aka yanka ta da sauri don kada ta yi mushe.

Dabi’un Bafulatani makiyayi tabbas sun nuna cewa mutum ne mai yin kaffa-kaffa da duk wani bala’i da ka iya afka wa dabbobin sa. Ya na kokarin kauce wa duk wata fitina da za ta iya haddasa masa asarar ko da dabba guda daya ce.

Kamar shekaru 30 da suka wuce abin da ya yi baya can, Fulani makiyaya matsotara ne – amma tsoron hukuma, musammam dan sanda. Ko a kan babur suka ga an gilma da dan sanda an bi ta rugar su, za ka ga sun sheka a guje cikin jeji.

Baya ga wannan, akwai su da tarairayar bakon da ya same su har rugar su. Su da matan su duk ba su dogara da sai wani ya ba su wani abu, ko ya taimake su don su kawar da kananan matsalolin su ba. Matan su kan shigo gari su na sayar da nono da mai. Wani lokacin kuma su na shigowa gari duke da kwayayen zabi su sayar.

Me ya sa makiyayin da ke hijira daga wannan jiha zuwa waccan tare da daruruwan dabbobin da ba ya so ko kuda ya taba su, aka wayi gari shi ne zai yi kisa har ya gudu ya bar dabbobin sa? Anya kuwa?!

TSAKANIN MAKIYAYA DA FULANI:

A shekarun baya kamar 40 abin da ya yi baya, mun san lokacin da Fulani ba su bin ko’ina idan su na kaura daga nan zuwa can, sai dai kawai gwadaben su, wato burtali. Sannu a hankali mahukunta da masu gari duk suka sayar da wannan gwadabe da burtali ga manoma, ta yadda makiyaya ba su da hanyar bi su rika kaura ko hijira, tilas sai sun yi ratse cikin gonaki.

ASALI DA TUSHEN FADAN MAKIYAYA DA MOMA:

Tun cikin 1978 na fara fahimtar inda aka fara samun matsala a tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma. A lokacin ina karami a kauye, idan kaka ta yi, yawancin manoma su kan ki kwashe amfanin gonar su da wuri. Za su tattara shi wuri daya a cikin gona, amma ba za su kwashe su kai gida ba. Maimakon haka, sai su tattara gero, dawa ko gyada a wuri daya a tsakiyar gona, su yi zabaro na karan dawa ko karan gero su rufe.

Wasu matasan kauye za su tara amfanin gonar na su a gona, su rufe, sai su fantsama cikin garuruwa yawon ci-rani. Haka za a dauki tsawon lokaci, har rani ya shigo lokacin da ya kamata a fara sakin dabbobin gida irin su akuya, tunkiya da jakai su na fita daji kiwo sakaka, ba tare da makiyayi tare da su ba.

Kafin wannan lokaci, Dagatan kauye da masu Unguwanni kan sa a yi yekuwa ana tunanar da manoma cewa kowa ya kwashe amfanin gonar sa, domin za a bada umarnin a saki dabbobi su fita kiwo, saboda rani ya yi, abincin dabbobi ya fara karanci.

To daga karshe kuma sai a yi yekuwar bada umarnin a saki dabbobi su fita kiwo, sakaka, ba tare da wani makiyayi na biye da su ba:

YEKUWA:
“Sarki ya aiko ni,
Hakimi ya aiko ni,
Maigari ya aiko ni,
Abin da su ka ce a fada muku jama’a,
Duk daukacin magidanci duka,
Idan Allah ya tashe mu gobe lafiya,
Da mai akuya da mai saniya da mai tunkiya,
Kowa ya balle bisashe nai.”

Watau wannan ballewar ta na nufin a balle dabbar ka daga tirke, ka sake ta ta rika fita jeji da gonaki ta na kiwo da kan ta, ba tare da makiyayi ba. Za a saki akuya ko tinkiya su rankaya jeji su na kiwo. Idan rana ta take tsaka wajen daya na rana, za su dawo gida su sha ruwa, kuma su koma jeji kiwo. Daga nan ba za su koma ba, har sai rana ta fara disashewa, magriba za kusa, sannan za su koma gida, a kama kowace, a daure, sai kuma gobe da safe.

MATSALAR MANOMI:

A wannan lokacin, akan samu manoma masu kunnen-kashi, wadanda ko da sun kwashe amfanin gonar su sun kai gida, to za su bar karan gero da karan dawa da ganyen gyada ko kuma kowar wake da harawa a gona. Sai su tattara a wuri daya, su yi zabaro, sannan su bi su layyace shi da darni na kaya mai tsini, don kada dabbobi su cinye musu.

AMBALIYAR FULANIN BAKOLO DA BARAROJI:

Yawancin wadannan Fulani da Jamhuriyar Nijar su ke nausowa daga Arewa su dumfaro kudu. Sun fi Fulanin Nijeriya yawan shanu da tumaki da awaki. Idan za su wuce, kwan su da kwarkwatar su suke tasowa gaba daya, ba su barin kowa.

Hatta turmin daka da tabarya da muciya da maburkin miya duk ba su bari. Saboda duk inda su ka sauka su ka yada zango, to nan ne gida a wurin su.

Wadannan Fulani mafadata ne sosai, amma kuma sun iya zaman lafiya da mutane. Duk da irin matsoloncin su, a duk inda su ka yada zango, su kan saba da jama’ar da ke zaune cikin kauyukan da ke kusa da sansanonin su. Idan biki ko suna ya kama a cikin gari su kan shigo a yi mu’amala tare da su.Idan suka tashi za su matsa gaba, su kan yi wa ‘ya’yan abokan zumuncin su kyautar dan tinkiya namiji ko mace.

Su ne irin Fulanin nan da z aka ga namiji da kitso ga kuma karafuna da sulalla ya dauka kowace kaikainiyar kitson. Ko kuma ka gan su da tukkuwa a tsakiyar kai.

Wadannan Fulani kan rika tafiya da makamai, da su ka hada da takubba, manyan sanduna, zunduma-zunduman wukake, kibiya da kuma irin bindigar takar nan ta maharba. Me ya sa su ke tafiya da wadannan makaman? Saboda namun dajin da ke kai wa dabbobin su farmaki da tsakar dare, kamar kura da kyarkeci masu fizgar tinkiya ko akuya su tsere da su. Sai kuma manyan barayin dare, wadanda ke sadadawa da tsakar dare su na satar musu shanu. Sau da yawa kuma sun a fama da hatsabiban matasan karkara masu bin dare sun a kokarin su yi wa matan auren su ko ’yan matan cikin su fyade.

Idan fada yah ado ku da su, to ba su da mantuwa, kuma ba su yafewa, musamman idan kun kashe musu iyaye ko matasan su.

YA AKE HUKUNTA BARNAR MAKIYAYA A BAYA?:

A shekarun baya masu yawa, abin da mu ka sani shi ne idan saniya ko tumakin makiyayan Fulaninmu na gida ko Bakolo ko Bararoji su ka yi barna, sai mai gona ya kai kara a wurin mai unguwa ko Dagacin gundumar su kai-tsaye. Dagaci zai aika a kira bban Ardon cikin wadannan makiyaya, ya ce ya zo tare da mai shanun da su ka yi wa mai gona barna.

A nan take Dagaci zai ci tarar makiyayin nan. Shi kuma zai ce a lamunce shi ya kai akuya ko tinkiya kasuwa ya sayar, domin ya biya tarar da aka yi masa. Idan ya kawo tara, Dagaci zai kira mai gona ya ba shi, shi ma ya dan yagi nasa rabon.

Inda aka fara samun matsala, shi ne daga lokacin da ’yan sanda su ka gane cewa sasanta rikici tsakanin makiyaya da manoma hanya ce ta samun kudi. Sai su ka kwace shari’ar Fulani makiyaya da manoma daga hannun Dagatai, aka waske ofishin ’yan sanda ana yi a can.

Daga karshe, maimakon a rika samun maslaha, sai manomi ya fahimci shi da aka yi wa barna, kara tabka asara ma kawai ya ke yi a hannun ’yan sanda, ko kuma a biya shi tarar da aka yi wa makiyayi, amma kudin su makale a ofishin ‘yan sanda. A gefe daya shi ma makiyayi sai ya karke ga biyan makudan kudade a kan barnar da ba ta kai naira dubu biyu ba, ya yi asarar sama da dubu goma, alal misali.

KOWA TASA TA FISSHE SHI:

Daga nan sai bangarorin biyu su ka daina neman hukuma ko jami’an tsaro su na shiga cikin sabanin da ke afkuwa a tsakanin su. Idan makiyayi ya yi sakacin karya doka, ya bari dabbar sa ta shiga gona ta ci amfanin gonar da bai wuce naira dubu daya ba, shi kuma manomi zai karya doka, ya kashe wannan akuya ko tinkiya ko saniya, ko da kuwa kudin su ya ninka kudin amfanin gonar da aka ci sau goma.

Akan kuma samu matsalar inda mai gona zai zuba ko dai guba ko kuma wani abu da dabbobin makiyayi idan sun ci za su mutu. To wannan da kuma dalilan da na bayyana can sama, kan sa shi ma makiyayi ya yi shirin daukar fansa, ta hanyar karya doka. Ya bi dare ko rana, ya iske mai gona ya hau shi da duka da rasa, har ta kai ga kisa idan da karar-kwana.

RINCABEWAR FADAN MAKIYA DA MANOMA A AREWA TA TSAKIYA:

Kafin 2010, akan samu rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma, amma dai bai yi muni sosai ba. Magana ta gaskiya ita ce, daga 2010 ne wannan musiba ta munana, kuma siyasa ce ta haifar da hakan, har ya munana ya rikide zuwa rikici na kabilanci da addinanci.

Kuskuren Da Aka Tafka A Filato:

Cikin 2010 da kuma 2011 an yi mummunan kashe-kashe a Jijar Filato. Rikicin nan ya samo asali ne daga zaben Shugaban Karamar Hukumar Jos ta Arewa, wanda ya haddasa fada tsakanin Hausawa da ‘yan Kabilar Birom. Bayan an kashe Hausawa birjik, sai kuma aka rika bi cikin jeji ana kashe Fulani, ba ji ba gani kuma ana kashe musu shanu tare da sace daruruwan shanun.

Bafulatanin da ke kiwo a daji, babu ruwan sa da zabe, babu ruwan sa da yankar rajista, balle a gan shi cikin gari ana karankatakaliyar kamfe da shi.

Akasarin su ma ba su san ko kansilan su ba, ballanatana a karkashin wace karamar hukuma su ke.

Sai aka shiga yanayin da bayan kura ta lafa, an kashe daruruwan rayukan shanu da na mutane da sauran dabbobi, Fulani sun kai kara cewa ga shanun su can a gidajen ‘yan kabilar Biron a kullum ana yankawa ana dagargazar gara da naman shanu da tumakan su. Amma hukuma ba ta yi komai a kai ba.

Aka wayi gari wanda ke da alade biyu a gidan sa, sai ka gan shi da shahu byar ko goma, sannan kuma ga tukamai da raguna. Su kuma Fulani gas u can a gefe sun a zaman makokin kisan ’yan uwan su da jimamin asarar da su ka tafka.

Fadan zaben 2011 ya sake ritsawa da wasu Fulani a yawan su ma baki ne, ba ‘yan Nijeriya ba, a cikin Kudancin Kaduna, inda a Zonkwa kawai aka kashe daruruwan Hausawa. Su kuma Fulanin nan duk wanda ka gani, ba shi kadai ke da shanun ba.

Yawancin masu tulin shanun su na gida.

Wannan ta sa sun rika aikawa da goron gayyata daukar fansa a duk inda aka karkashe su musamman a wadancan fadace-fadacen siyasa.

KISAN FULANI A JIHAR BENUWAI

Lokacin da ina Editan RARIYA bazan manta ba, cikin 2013, kungiyar Fulani sun taba kawo ziyara ofishin mu a Abuja, domin su nuna kukan su dangane da yadda ake yi musu kisan-kiyashi a jihar Benuwai, tare da karkashe dabbobin su, amma gwamnati ba ta dauki matakin komai ba.

Fulanin sun yi gangami tare da tulin matan da aka bari su na takabar kashe mazan su da aka yi a jihar Benuwai. Haka kuma sun zo da dandazon kwanyamin kananan yara wadanda aka kashe iyayen su aka bar su cikin maraici da kuncin rayuwa.

Ba a nan abin ya tsaya ba. Sun kuma je da tulin daruruwan hotunan gawarwakin shanun su da aka kashe, tare da adadin wadanda aka sace.

Yawan dandazon Fulanin ya sa tilasa mu ka bada shawara a tafi hedikwatar Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa (NUJ) da ke Jabi, Abuja, domin su gabatar da taron manema labarai a can.

Wasu daga cikin su ma a mota ta na dauke su zuwa ofishin kungiyar ta ‘yan jarida.

A wurin suka yi jawabin irin kisan da ake yi musu a Benuwai, tare da nuna wa ‘yan jarida tulin hotunan wadanda aka karkashe da wadanda aka ji wa ciwo, da kuma yin bayanin yadda ake sace musu shanu, su na ji sun a gani a rika loda shanun su a manyan motoci ana tafiya Aba da Anacha ana sayar da su arha takyaf.

YADDA JARIDU KE HADA FULANI DA MAKIYAYA FADA:

A kasar nan an rigaya an cusa kiyayya ga Fulani makiyaya a kafafen yada labarai.

Idan za a bi dare a cikin kudancin Kaduna da Nasarawa da Filato da Benuwai da Taraba ana kashe Fulani, to jaridun Kudu ba za su dauki abin har su yayata shi ba.

Sai ranar da Fulani suka gaji da jiran hukuma ta yi wani abu, idan ba ta yi ba, sai suka bi dare su dauki fansa, to ranar ne duk jaridu da kafafen yada labarai na kudancin kasar nan za su cika jama’a da labaran Fulani sun yi kisa.

Game-garin mutanen da ba a sanar irin barnar da aka yi wa Fulani kafin su dauki fansa ba, sai su rika kara cusa wa kan su da ’ya’yan su kiyayya da tsanar Fulani. An karkashe Fulani makiyaya da daruruwan dabbobi da yawa a Benuwai da Taraba da Filato da Adamawa da Nasarawa da Kudancin Kaduna. Duk wannan kisan da aka yi musu bai girgiza marubuta da ’yan katsalandan din kishin kabilar kudu ba, sai kisan da Fulani su ka yi a Benuwai na kwana-kwanan nan.

Ya kamata gidajen jaridu su sani cewa, idan za a shekara 100 suna danne kisan da ake yi wa Fulani ba su bayyanawa, to ai su Fulanin sun san cewa an kashe su. Sau da dama fadace-fadacen nan na ramuwar-gayyar daukar fansan kisan da aka yi ne baya, shekaru daya, biyu, uku kai ko ma biyar baya.

WATA MATSALAR JARIDUN NIJERIYA:

Sau da yawa saboda kokarin dankwafar da Fulani da kuma rufe barnar da ake musu, sun daina ganin Fulani a matsayin wasu mutane sahihai. Haka kuma ba su dauki shanu da daraja ba. Idan aka kashe wa Bafulatani shanu 15, wadanda kudin su ya kai naira milyan biyu da rabi, to jaridu ba za su dauki labarin da muhimmanci ba.

Sai ranar da Fulani su ka bi dare suka kone bukkoki biyar na wasu kabilun Tivi ko Birom ko Kaje ko Katab, wadanda bukka daya tal za a iya gina ta da naira dubu 20,000, to sannan ne aka samu labarin bugawa ana yayatawa duk duniya ta sani.

RAINI TSAKANIN FULANI DA SAURAN KABILI:

Fulani wasu shu’uman kabila ne a Afrika ta Yamma. Ga shi dai kowace kabila ta raina su, amma kuma idan aka yi duba da idon basira, sai a ga kusan sun fi kowace kabila. Fulani sun yi shugabancin kasashe da dama a Afrika ta Yamma, ciki har da Nijeriya. Kuma har yanzu su na shugabancin wasashe ba daya ba, ba kuma biyu ba a Afrika ta Yamma.

A zaman yanzu, gwamnonin da ka yi Arewacin Nijeriya daga siyasar 1999 zuwa yau kan wadanda ke mulki, duk Fulani sun fi yawa. Haka ministoci, musammamn ma lokacin Jamhuriya ta Farko.

Ana yin sakaci sosai a kasar nan, da ba a maida hankali kan mummunar barnar da ake yi wa Fulani makiyaya. Cikin shekara biyar da ta gabata zuwa yau, an sace dubban shanun Fulani a dazukan Katsina, Zamfara da Birnin Gwari. An kashe daruruwan jama’a tare kona musu matsugunnai. Amma kamar ma an manta da wannan mummunan kassarawa da aka yi kuma ake ci gaba da yi musu.

KOWANE GAUTA JA NE…

Babban sakacin da aka yi na kin maida hankali sosai ga barnar da ake wa Fulani musamman satar shanun su da karkashe musu dabbobi a Katsina da Zamfara da Kaduna, ya sa an dauki munanan laifuka da barna daga cikin birni an kai a gaban wasu Fulanin har rugar su an kasa a faifai su na ganin yadda ake yi.

A yau an wayi gari matasan Fualani sun fi yawa a larnar tare hanya ana garkuwa da mutnae a kan manyan titina, musamman a tsakanin Abuja da Kaduna, Abuja da Minna da Kaduna zuwa Birnin Gwari.

A lokacin da ake guguwar kwashe wa Fulani shanu a dajin Zamfara da Katsina da Birnin Gwari, kiri-kiri da rana tsaka barayi za su rika ajiye dogayen motoci ana lodin shanun sata ana nausawa da su kudu a sayar.

MU SHEKARA TAMBAYAR JUNA:

Dama Bahaushe ya ce “idan ka ji ana sa-toka-sa-katsi, to baba ce ba ta ji ba. Sai mu tambayi junan mu. Shin kashe Fulani ne ba babbar matsala ba, ko kashe manoma? Shin kashe dabbobi ne ba babbar matsala ba, ko kuwa banka wa kauyuka wuta? Shin fara kai hari a yi kisa ne laifi ne? shin ita ma ramuwar gayya laifi ce? Tare manyan titina ana garkuwa da mutane laifi ne? Shin duk wadannan laifuka manyan matsaloli ne ko kuwa? Idan duk mun yarda cewa matsaloli ne, to ta yaya za a magance su?
Amsa a nan ita ce, daga tushe za a dauko gyaran, ba daga sama ba!

Share.

game da Author