Tsohuwar Ministar Ilimi, Oby Ezekwesili, ta bayyana cewa sabon tsarin siyasar da ta fito da shi, shi ne tabbatar da cewa manyan jam’iyyun siyasar nan biyu, APC da PDP, sun yi zubar-gado, kowanen su ya fadi zaben gwamnnoni da na shugaban kasa a 2019.
Ezekwesili, wadda ta ke daya daga cikin shugabannin #Bring BackOurGirls, masu rajin gaggauta ceto ‘yan matan Chibok daga hannun Boko Haram, ta ce shirin na ta ya danganci daukar duk wani mataki da zai hana wadannan jam’iyyun gungun mabarnata, maciya amana wadanda su ka yi wa kasar nan tarnaki da dabaibayi, su ka hana ta ci gaba.
“Haba jama’a! Mun gaji da su haka nan fa.” Haka Oby ta rubuta a soshiyal midiya, cikin shafin ta na Twitter, mai suna @obyezeks.
“Ajanda ita ce zan yi kamfen bakin-rai-bakin-fama domin na tabbatar dan PDP da dan APC ba su nasara a kan mukaman da su ka tsaya a kowace irin takara a zaben 2019 ba, sai fa a inda kawai na ga an tsaida mutumin kirki, nagarri, to wannan shi ne nawa.
“Duk inda na ga an tsayar da mutumin kwarai, to wannan ina can, ammaa ba zan bi ko na goya baya a zabi mutumin banza ba.
“Ina fatan a kawo karshen mulkin wasu ‘yan kalilan da su ka hana ruwa gudu, shekara da shekaru a kasar nan da su ake damawa kuma ake shanyewa.