Mutane da dama Boko Haram suka yi garkuwa da su a harin Adamawa

0

A yau Talata ne wasu mazauna kauyen Pallam dake karamar hukumar Madagali jihar Adamawa suka shaida wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram sun kawo hari kauyen da karfe 11 na daren Litini inda mutane da dama suka rasa rayukan su sannan aka yi garkuwa da wasu da ake zaton duk maza ne.

Wani cikin mazauna kauyen Pallam, Abamu Japhet ya sanar wa wakilin mu cewa da kyar ya tsira da ran sa a wannan tashin hankali.

Ya ce Boko Haram sun yi sama ada awa biya suna yin abin da suka ga dama a kauyen babu wani taimako da daga jami’an tsaro ko daya.

Shima dan majalisar wakilai wanda ke wakiltan yankunan Madagali da Michika Adamu Kamale ya tabbatar da harin inda ya ce maharan sun kashe mutane, sun kona gidajen mutane da na dabobbi da dama a kauyen.

Daga karshe kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Othman Abubakar ya fada wa wakilin mu cewa ba shi da cikakken bayanai kan harin da aka kai wannan kauyen amma ya ce da zaran ya sami tabbacin haka zai nemi shi.

Share.

game da Author