Muna rokon Makarfi ya fito takarar shugabancin Kasar nan – PDP

0

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna tayi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi tayin fitowa takarar shugabancin Nageriya.

Tsohon gwamnan jihar, Ramalan Yero ne ya bayyana haka a taron gangamin ‘ya’yan jam’iyyar a Kaduna.

Yero yace ganin yadda Makarfi ya rike jam’iyyar PDP a lokacin da take cikin halin kaka-nikaya nuni ne cewa Najeriya ma ba zata gagare shi ba.

” Makarfi ne yafi dacewa da kujerar shugabancin Najeriya. Muna rokon sa da ya amsa wannan kira ya fito ya nemi kujerar shugabancin kasar nan, za mu mara masa baya 100 bisa 100.

Shugaban jam’iyyar na jihar Kaduna, Hassan Hyat ya yaba wa ‘ya’yan jam’iyyar ganin yadda suka fito kwan su da kwarkwatan su suka halarci taron.

Ya ce jam’iyyar na shiri sosai don tunkarar 2019.

Share.

game da Author