Muna neman karin tsaro daga hare-haren ‘yan Kabilar Bachama – Kungiyar Fulani

0

Kungiyar Fulani na ‘Mobgal Kautal Hore Fulbe’ dake kananan hukumomin Numan, Demsa da Lamurde sun koka kan yadda ake wa ‘yan uwansu Fulani kisan gila a jihar Adamawa.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnanti da ta samar musu da tsaro a wadannan yankuna saboda rashin yin haka zai sa dole su nemi hanyoyin kare kan su da kan su.

Idan ba a manta ba a shekarar 2017 an sace mutane sama da 100 a wadannan yankuna sannan a cikin watannin da suka gabata an sace sama da shanu 500 duk daga wadannan yankuna.

Bayan haka shugaban kungiyan makiyaya ‘Miyetti Allah’ reshen arewa maso gabas Mafindi Umaru Danburam yace tun da aka sanar da cewa garin Numan ya gagari Fulani zama ‘yan Kabilar Bachama suka fara farautar duk bafulatanin da ke zama a wadannan yankuna.

” A yanzu haka muna da labarin kisan da ‘yan kabilar Bachama suka yi wa wasu makiyaya uku a lokacin da suke kiwo da wani wanzami a kauyen Anguwar Green. Bayan haka kuma ‘yan kabilar Bachama din suna sace mutanen mu a hanyoyin Kpasham, Mararraban Dong, Gyawana, da Lamurde-Tigno.”

Daga karshe kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Othman Abubakar ya ayyukan da ‘yan kabilar Bachama suke yi musamman na shingen da suke sace makiyayan.

Ya kuma kara da cewa sun sami sunayen wasu ‘yan Kabilar Bachama din da ake zargin su da kisan makiyaya uku da wanzami sannan ya tabbatar da cewa suna iya kokarin su domin ganin sun kama duk wadanda suke da hannu cikin tada rikicin wannan yankunan.

Share.

game da Author