Kungiyar Malamai reshen jihar Kaduna ta sanar da janye yajin aikin da malaman makarantun Firamare da Sakandare su ka shiga sanadiyyar koran dakikan malamai da gwamnatin jihar tayi.
Shugaban kungiyar Audi Anna, ya ce kungiyar ta cimma wannan matsaya ne bayan ganawa da suka yi da gwamnatin jihar da kuma sassautawa da gwamna El-Rufai yayi cewa duk wani malami da aka kora zai iya sake neman aikin malunta a jihar.
Kungiyar ta ce hakan da gwamnan yayi abune mai kyau cewa zai kara ba malaman da suka fadi jarabawar gwajin daman sake neman aiki a jihar kuma idan sun ci a dauke su aiki.
Idan ba a manta ba gwamna Nasir El-Rufai a ganawa da yayi da shugabannin kananan hukumomin jihar da sakatarorin ilimi na jihar ya ce gwamnati ba za tayi amai ta lashe ba. Tana nan kan bakan ta na lallai wadanda suka fadi jarabawar gwaji a sallame su sannan sabbin malamai da za a dauka za su fara aiki ne daga watan Fabrairu.
Daga karshe, Audi ya yabawa malaman jihar da kuma kungiyar kwadago kan mara musu baya da suka yi a lokacin wannan gwagwarmaya.