Mun kakkabe Boko Haram kakaf, inji Buratai

0

Babban Hafsan Hafsoshin Askarawan Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa tabbas su na nan kan bakan su na cewa an kakkabe Boko Haram kakaf.

Ya yi wannan jawabi ne a jiya Lahadi, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari da jami’an sa su ka rika furtawa watannin baya cewa an kakkabe Boko Haram.

To sai dai kuma masu sukar gwamnatin Buhari, ‘yan adawa da sauran ‘yan gaji-gani ba su yarda da irin wadannan furucin ba. Sun rika bayyana irin dauki ba dadin da ake yi tsakanin sojoji da mambobin Boko Haram a yanzu.

Baya ga kazamin yakin da ake fafatawa da su, masu sukar gwamnatin na ganin cewa idan har da gaske ne an kakkabe Boko Haram, to don me gwamnatin Buhari za ta nemi kashe naira dala bilyan daya wajen yaki da Boko Haram?

Sai dai a ranar Lahadi, yayin da ya ke jawabi a wurin bikin Ranar Tunawa Da ‘Yan Mazan Jiya, a Maiduri, Buratai ya ce an yi nasara kan Boko Haram.

David Ahmadu ne, Kwamandan Horas Da Sojoji na Hedikwatar Askarawan Kasar nan ya wakilci Buratai a wurin bikin.

Ahmadu ya zayyana nasarorin da aka samu kan Boko Haram a baya-bayan nan. Sannan kuma ya koka da yadda Boko Haram suka rika horas da kananan yara su na tura su yin harin kunar-bakin-wake.

Share.

game da Author