TAKAICIN SHUGABA BUHARI:
Ina mai takaicin ganin yadda wasu masu muguwar aniya su ka hana ‘yan Nijeriya gudanar da shagulgulan Kirsimeti da Hutun Sabuwar Shekara a cikin walwala, ta hanyar kuntata wa jama’a tsada sa karancin man fetur. Sun jefa jama’a cikin kunci da tsadar kudaden mota a lokacin zirga-zirga zuwa hutun Kirsimeti.
Ba za mu aminta da irin wannan zagon kasa ba, domin tuni Hukumar NNPC ta dauki kwararan matakan wadatar da kasar nan da mai. Sannan kuma za a binciko wadanda ke da hannu domin daukar mataki a kan su yadda hakan ba zai sake faruwa ba.
HOBBASAN GYARAN TITINAN MOTOCI DA NA JIRAGEN KASA:
1. Ana ci gaba da titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Kano. Titin zai isa Ibadan nan da 2019, wanda a kowace shekara zai kwashi fasinjoji milyan biyu da kuma tan milyan biyar na lodin kaya.
2. Za a kammala aikin titin jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna can gaba wajen karshen 2019. Ya zuwa karshen 2021 za a hade hanyoyin ta yadda za a samu titin ya karasa kai-tsaye daga Arewa zuwa Kudu.
3. Nan da ranar Alhamis mai zuwa ce za a kara wa titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna wasu tarago da kuma kan jirgi biyu, ta yadda za a rika jigilar fasinjoji akalla milyan daya a kowace shekara.
4. Na rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin titin jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri, ya zarce Aba, ya hada da Owerri, Umuahia, Enugu, Awka, Abakaliki, Makurdi, Lafia, Jos, Bauchi, Gombe, Yola ya zarce har Damaturu.
4. Ana nan ana tattauna batun aikin tirin jiragen kasa daga Kano zuwa Maradi cikin Jamhuriyar Nijar, zai biyo ta Kazaure, Daura, Katsina, Jibia zuwa Maradi.
Na Lagos zuwa Calabar shi ma ya na kan hanya. Nan da shekaru kalilan za hade garuruwan kasar nan da titinan jiragen kasa.
5. Shi ma aikin titin jirgin kasa na zirga-zirgar cikin kwaryar Abuja da kewayen ta an kusa kammala shi. Yanzu aikin ya kai kashi 98% bisa 100%. Lokacin da mu ka hau ya na a kashi 64% bisa 100% ne.
HARAMAR GYARAN TITINAN MOTOCI:
1. Mun umarci Hukumar Gyara da Kula da Titina, FERMA da ta gyara titina 44 na cikin kasar nan, a cikin makonni 12.
2. Za mu gina titina 25 da tsabar kudi har naira bilyan 100 a karkashin tsarin SUKUK. Wadannan titina sun hada da:
a. Oyo – Ogbomosho,
b. Ofusu – Ore – Ajebandele – Shagamu,
c. Yenagoa – Fatakwal,
d. Onitsha -Enugu,
e. Yenagoa zuwa Otuoke,
f. By-pass na Gabacin Kaduna,
g. Titin Kano zuwa Maiduguri,
h. Titin Abuja zuwa Lokaja zuwa hanyar Benin,
I. Titin Suleja zuwa Minna.
2. Gwamnati ta amince da sake gina titin Abuja–Kaduna-Zaria-Kano. Kwanan nan za a fara kuma ana sa ran kammalawa cikin 2019.
HASKE MAGANIN DUHU:
1. Ana kan aikin inganta hasken lantarki na Pay Assurance Guarantee Scheme, da aka fara tun cikin watan Janairu, 2016.
2. A yanzu Nijeriya na samun karfin hasken lantarki har Miga Wat 7000. Ranar 8 Ga Disamba ne aka samu har 5,155mw.
3. An fara samu hasken lantarki Katsina na 10mw, za a kammala aikin hasken lantarki na Zungeru nan da 2019. An kusa kusa kammala aikin samar da wuta na Gurara, Kashimbilla da Kaduna.
4. Gagarimin aikin samar da hasken lantarki na Mambilla na kan hanya. Tun shekaru 40 baya ake ta shelar za a yi, amma mu mun fara aikin, wanda zai samar da 3,050mw. Za a kammala shi cikin 2013.]
6. Akwai wasu karin ayyukan a Ekpene, Aba, Alagbon, Ajah, Ejigbo, Funtua da Zaria.
NOMA YANKE TALAUCI:
Shekaru biyu da suka gabata na yi kira da a koma gona a rungumi noma gadan-gadan. Ina matukar farin ciki ganin yadda a kakar bana yadda manoma suka huce haushin su. Don haka za mu hana shigo da shinkafa daga kasashen waje. Kowa zai koma cin shinkafa ta cikin gida domin mu gina kan mu kuma mu gina jikin mu.
GABATOWAR ZABEN 2019:
Ganin yadda zaben 2019 ke kusantowa, ya kamata ‘yan siyasa su guji kalaman batunci da haddasa kiyayyar kabilanci ko addinanci. Sai mun kauce wa haka za mu iya zamantakewa a cikin lumana.
INEC TA YI RAWAR GANI:
Ya kamata mu kara wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, kwarin guiwa, ganin yadda ayyukan hukumar na yadda ta gudanar da zabukan cike gurabu a cikin 2017 ya yi kyau da inganci sosai.
An gudanar da zabuka da dama ba tare da tashe-tashen hankula ba, kuma dukkan sakamakon zabukan sun tabbatar da an yi adalci ga kowane dan takara.
GARKUWA DA JAMA’A:
Mun kara tashi haikan wajen kakkabe wannan matsalar wajen kara tsananta ayyukan jami’an tsaro da kuma yin hukunci mai tsanani ga duk masu aika wannan mummunar aika-aika.
GODIYA DA FATAN ALHERI – ga dukkan ‘yan Nijeriya musamman wadanda su ka yi min addu’ar samun sauki da lafiya a lokacin da na kwanta jiyya cikin shekarar da ta gabata.
Ina yi wa kowa Murnar Shigowar Sabuwar Shekara.