Matafiya Turai 200 ciki har da ’yan Najeriya sun nutse a teku

0

Kimanin masu hijira zuwa zuwa kasashen Italiya da Spain su 200, cikin su har da ‘yan Najeriya da dama su ka nutse a cikin Tekun Mediterranean a ranar jajiribirin Sabuwar Shekara.

Hukumar Kula da Hakkin Masu Hijira ta duniya ce ta bayyana wannan adadin.

Jamai’ar Yada Labaran Hukumar, da ke Libya, Christine Petre ce ta bayyana cewa jiragen kwale-kwalen da ke dauke da su sun tashi daga tashar jiragen ruwa ta garin Azzawiyah da Al Khums daga Libya.

“Akasarin wadanda suka tsira sun fito ne daga kasashen Afrika, ciki har da Senegal, Mali da Najeriya. Masu tsaron gabar tekun Libya sun ce a ciki akwai mutane takwas ‘yan asalin Bangladesh sai wasu biyu daga Pakistan.

Jami’an sun ce har yanzu tun bayan da jirgin ya kife, ba a sake ji ko ganin motsin fasinjoji kimanin 100 ba.

Share.

game da Author