Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba ta tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane sun kashe Dan majalisar Jihar Taraba bayan sun tsare shi kwanaki da dama a hannun su.
Kakakin ‘yan sanda mai suna David Misal, ya ce masu garkuwar sun kashe Hon. Hosea Ibi, wanda ke wakiltar Karamar Hukumar Takum 1, a Majalisar Dokokin jihar.
Ya ce an tsinci gawar Ibi a yau litinin.
“Babban abin takaici shi ne, duk da irin kokarin da mu ka yi domin cim ma masu garkuwar da su ka sace shi, amma sai gawar sa mu ka tsinta a kan hanyar Kashinbila. Amma hakan ba zai gajiyar da mu ba, har sai mun gano ko su wa ne su ka aikata hakan.
“Saboda haka mu na kira ga jama’a su ba mu duk wani bayanin da su ka sani, wanda zai iya kai mu ga gano wadannan makasan.” Inji kakakin jami’an tsaron.
Wata majiya daga iyalin mamacin ta bayyana cewa sun rika yin waya da masu garkuwar, inda suka nemi sai a biya su naira milyan 100.
Majiyar ta ce kuma sun rika yin magana da dan majalisar domin a tabbatar musu da cewa ya na da rai, bai mutu ba, amma kuma daga baya suka kashe shi.
Sai dai kuma wata majiya ta tabbatar da cewa a bisa dukkan alamu, a yadda su ka samu gawar dan majalisar, to an kashe shi ne kwanaki biyu da su ka gabata.