Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya sanar da cewa wadanda suka sace sarkin Ikulu Yohanna Kukah sun sake shi.
Yohanna Kukah shine sarkin Ikulu sannan danuwa ne ga Rabaren Hassan Kukah.
Ya fadi haka ne ranar Alhamis da yake zantawa da manema labarai, sannan ya kara da cewa masu garkuwan sun saki Yohanna ne da misalin karfe 3 na yamma.
Aliyu yace ba zai iya tabbatarwa ko an biya kudin fansa kafin a sake shi ko a’a, sai dai jami’an sa sun fantsama don ganin sun kamo wadanda suka yi garkuwa da sarkin.
Ya ce an sako Yohanna batare da ya sami rauni a jikin sa ba sannan tuni ya koma wajen iyalan sa.