Mutane a zahiri na kallon yadda jami’an hukumomin tsaron gwamnatin Muhammadu Buhari ke kazar-kazar, karakaina da kamo wannan, cafko wancan, duk a kokarin su na cika-aikin gudanar da tsaro ga gwamnatin Buhari, ashe ba a sani ba a tsakanin su babu komai daga yankan-baya sai cin-dunduniya sai kuma karo-da-karo, musamman tunda dukkanin su manyan raguna ne.
PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo muku irin yadda NIA, SSS da EFCC ke karo da juna a cikin duhu, yayin da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari da ubangidan jami’an tsaron, Janar Monguno ke hararar juna a cikin haske ko a duhu. Wane damu Daura shugaban SSS ke damalwalawa? Me ya sa Magu ya zame wa wasu ogogin sa kadangaren bakin tulu? Ku biyo mu ku ji komai…
NIA: Yadda Aka Yi Wa Mohammed Dauda Dungun-kuturwa:
Tsohon Daraktan Riko na Hukumar Tsaro ta NIA, Mohammed Abba ya tashi da safiyar 9 Ga Janairu, 2018, a cikin nishadi da jin kan sa a matsayin wani babban jigo daga cikin jigajigan jami’an tsaron kasar nan. Ya shirya tsaf domin a ranar ce zai yi taron sirri na farko, shi da Shugaba Muhammadu Buhari, tun bayan da aka dauko shi daga Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Chadi, a cikin Oktoban da ya gabata.
An kira shi a wancan lokacin ne aka ce ba shi rikon hukumar tsaro ta NIA, wacce akasarin ayyukan ta duk leken asiri da kwakule-kwakule ne.
Idan ba a manta ba, tun cikin watan Afrilu da ya gabata ne hukumar NIA ta jefa kanta cikin barankyankyama da harkallar wasu kudi har dala miliyan 43, wadanda aka busa wa usur, aka gano a wani gida an kimshe su, a cikin unguwar Ikoyi da ke Lagos. Fallasa wadannan kudade ya janyo dakatar da shugaban hukumar na lokacin, Ayodele Oke.
Mu koma kan Dauda. A lokacin da ya fito daga ganawa da Shugaban Kasa, an ga fuskar sa cike da annashuwa da fara’a da cika ido, kai da ganin sa za ka yi tsammani ko albishir aka yi masa cewa an nada shi cikakken shugaban NIA, ya tashi daga shugabancin riko.
WANE NE DAUDA?
Wani kwararren jakadan huldar diflomasiyya ne da ke da kwarewa a fannin zakulo boyayyun masu laifin daka-dakar kudade. Majiya ta ce irin yadda ya san kabli da ba’adin masu tuggu, ya cancanta ya rike mukamin shugabancin NIA. Ga shi kuma dama a zaman sa Chadi, babu daren da jemage bai gani ba a rikici da siyasar diflomasiyyar yakin Boko Haram.
Aikin Dauda duk ya na a karkashin ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara a Fannin Tsaro, Babagana Munguno, wanda shi da Dauda din duk kabilar Kanuri ne. Sai dai kuma inda sakar ta cukurkude wa Dauda, majiya ta ce Munguno bai san za a dauki Dauda aiki ba, kuma babu wanda ma ya tuntube shi kafin a dauki Dauda aikin shugabancin NIA. Ashe kenan tilas Dauda ya rika taka-tsantsan kada garin gyaran gantsarwa ko doro, ya karya kugu.
Kwatagwangwamar SSS, EFCC DA SOJOJI:
Kwatsam a safiyar Laraba, 10 Ga Janairu, 2018, kwana daya bayan ganawar Dauda mai rikon shugabancin NIA a lokacin da shugaban kasa, sai yaran Lawan Daura, wato SSS suka shiga Defence Hause da ke Maitama, da nufin wai su na son ganin Abba Kyari, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.
Su ka ce sun je ne domin su kare Kyari daga wani kamu da Shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya turo jami’an sa su kama Kyari din.
Majiya mai tushe ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Shugaban SSS Lawan Daura ne da kan sa ya tura jami’an sa da umarnin cewa kada su sake su bari EFCC su kama Abba Kyari.
HARKALLAR NNPC: Ruwa Ba Ya Tsami Banza
Idan ba a manta ba, a farkon watan Oktoban da ya gabata, an fallasa wata cukumurda a kamfanin mai na NNPS, inda aka gano cewa an karkata wasu zunzurutun kudade har naira bilyan 50 zuwa cikin wasu asusu biyar da ke wasu bankuna biyar. Wannan kuwa a zahiri an karya doka, domin a ka’ida, a cikin Asusun Bai Daya (TSA) na gwamnatin tarayya ya kamata a zuba kudaden.
Wannan kakuduba ta kusa yi wa sunan Abba Kyari da mutuncin sa mummunan dameji, domin an ce shi ne ya bayar da umarnin a karkatar da kudin daga Asusun Bai Daya, TSA.
Masana kundin tuggun siyasar Abuja sun gutsuro mana cewa ofishin Shugaban Kasa da kuma ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara a Fannin Tsaro, Munguno, sun damu da wannan kakuduba ta naira bilyan 50 a NNPC, har ma su ka cunna EFCC a wurin domin ta yi bincike.
Sai dai kuma ita EFCC din ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa babu wanda ya cunna ta zuwa binciken wadannan kudade a NNPC.
LAWAN DAURA: Abokin Damo Guza:
Ganin yadda wannan kulli-kurciya ke ta karafkiya, sai nan da nan Shugaban SSS, Lawan Daura ya gaggauta tura jami’an sa domin su hana kama Abba Kyari. Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Wannan ne karo na biyu da Lawan Daura ke tura jami’an SSS su hana EFCC kama manyan jami’an gwamnati. Ranar 21 Ga Nuwamba, 2018, SSS sun tari gaban EFCC da fada, inda su ka yi babakere, su ka hana ta kama tsohon shugaban NIA, Ayo Oke da kuma tsohon shugaban hukumar SSS, Ita Ekpeyong.
Defence House: ‘Da Kare Da Biri’ Ta Wallare
Shi dai wannan katafaren wuri ne mai fadin gaske, da ke cikin Maitama, daidai tsallaken mahadar titin kusa da babban ofishin MTN na Abuja. Gidan ya na daya daga cikin gidajen saukar baki na Shugabn Kasa. Shi akan sa Buhari ya zauna cikin sa kafin a rantsar da shi. To a cikin sa ne gidajen Babagana Munguno da na Abba Kyari duk su ke, kuma gidan wannan ya na kallon na wancan.
Dangantaka tsakanin manyan jami’an gwamnatin Buhari biyu, Abba Kyari da Babagana Munguno ba ta da wani armashi ko kadan. Wata majiya ta ce, “su biyun kowa ta ciki na ciki.”
Duk su biyun ’yan kabilar Kanuri ne, ga su kuma su na a kololuwar kusanci da Buahri, sannan kuma ana ganin su biyun ne ke yi wa gwamnatin Buhari kitso-da-kwarkwata.
Artabun SSS Da SOJOJI A Gaban Gidan MUNGUNO
Yayin da jami’an SSS suka bazu birjik a kofar gidan Abba Kyari da ke kusa da gidan Munguno, a safiyar Larabar da ta gabata, wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa kowanen su ya rike da makamai.
An ce yayin da Munguno ya fito daga gida ya yi arba da gungun jamai’an SSS, sai ya bata rai, ya kalli hadiman sa a fusace ya ce, “wadancan kuma su wane ne?”
Nan take sai ga mota cike da karta-kartan sojoji, sun yi shirin fada, a bisa umarnin idan sun zo, su karbe bindigogin da ke hannun jami’an SSS.
An ce a nan dai aka yi ta surfa bakaken kalamai a tsakanin jami’an tsaron, daga bisani kuma hankali ya rinjayi fushi, dukkan jami’an su ka fice daga gidan.
MUNGUNO DA KYARI: Me Suka Shaida Wa Buhari?
Wata kwakkwarar majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa washegari ranar Alhamis Shugaba Buhari ya gana da Kyari da kuma Munguno, amma ba a lokaci daya ba. An ce ya gana da su ne domin ya sasanta sabanin da ke tsakanin su.
Wata Sabuwa Inji ’Yan Caca:
A ranar da Buahri ya gana da Munguno da Kyari, sai kuma ga takarda ta fito daga ofshin shugaban kasa ana sanar da cewa an nada Abubakar Rufai Ahmed a matsayin sabon shugaban hukumar tsaro ta NIA.
Rufai Abubakar wani mutum ne da aka tabbatar da cewa ya kware sosai wajen iya magana da yaren Faransa, Turanci da kuma Larabaci fiye da tunanin mai tunani. Ya taba yin aiki a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a ofishin ta na Afrika ta Yamma da ke Dakar, babban birnin kasar Senegal.
A bisa dukkan alamu an shiga gaban Munguno, domin an ce akwai wanda ya so a nada shugaban NIA kafin a bai wa Dauda riko, amma sai dai ya ji an nada Dauda ba da sanin sa ko an tuntube shi ba.
An ce shi kan sa Dauda sai dai ya ji labarin an canja shi a kafafen yada labarai.
IBRAHIM MAGU: Kadangaren Bakin Tulu
Babu abin da ake kwana ake tashi da shi a kololuwar tsaron kasar nan, kamar batun Shuagabn EFCC Ibrahim Magu. A lokacin hutun Kirsimeti, an ce Abba Kyari ya ja zugar Ministan Harkokin Cikin Gida, Bello Dambazau, Shugaban SSS, Lawan Daura da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, inda suka samu Buhari suka ba shi shawarar a canja Magu domin a cewar su, shi ne matsalar da ta hana gwamnatin sa tafiya daidai tare da Majalisar Tarayya. Sun ce saboda Magu ne Majalisar Dattawa ba ta saurin amincewa da batutuwan da shugaban kasa ke kaiwa a gaban ta.
An ce Buhari ya ba su shawara su je su gana da Maiataimakin sa, Osinbajo, domin shi kwararren masanin shari’a ne. Lokacin da su ka samu Osinbajo, ya nuna musu cewa cire Magu zai haifar da matsala, musamman ganin zaben 2019 na karatowa.
Osinbajo ya shaida musu cewa ana cire Magu aka canja shi da wani, to masu bakin magana cewa za su yi batun yaki da cin hanci da rashawa kuma ya zama busar-biri ko shillon-Bilya kenan.
Discussion about this post