Kungiyar malamai reshen jihar Kaduna ta yi kira ga malaman da gwamnatin jihar ta kora da su sake cika fom din neman aikin malunta a jihar.
Shugaban kungiyar Audu Amba, ya ce gwamna El-Rufai ya amince su kara neman aikin sannan su rubuta jarabawar gwaji, duk wanda ya samu nasara za a sake daukan sa aiki.
“El-Rufai ya umurci hukumar SUBEB na jihar ta bude kofa ga duk malamain da bai ci wannan gwaji da akayi a watan Julin 2017.
Ya ce duk da cewa sama da malamai 10,000 da suka fadi jarabawar sun sake nema har sun rubuta jarabawar da akayi na kwanakin baya, akwai sama da malamai 11,000 cikin su da basu cika sabon fom din neman aiki ba. Sannan ya kara da cewa za a fidda sunayen sabbin malamai nan da makonni masu zuwa.
” Za a tura malaman makarantun da a korar farko ya fi shafa.”