Majalisar Tarayya na fama da rashin kudi – Saraki

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa Majalisar Tarayya fama da halin karancin kudaden da suka wajaba su yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan su na tafiyar da majalisa.

Saraki ya yi korafin cewa, sabanin yadda jama’a ke kallon cewa ana labta wa majalisar kudade fiye da dimbin bukatun da suka wajaba, ya ce samun karuwar ayyukan gudanarwa a wannan zangon majalisa ta 8, ya sa su na fama da karancin kudade ainun.

A cikin wani bayani da Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Jaridu na Saraki ya fitar a ranar Laraba, Chucks Okocha ya ce Saraki ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara a ofishin Shugaba da kuma mambobin Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Tarayya, a matsugunin hukumar da ke Utako, Abuja.

A masa jawabin Shugaban Hukumar, Adamu Fika, ya nemi a samar wa hukumar tasa ofishi na dindindin a cikin Majalisar Tarayya.

Share.

game da Author